✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ayyana shugabannin riko a Mali

Tsohon ministan tsaro da shugaban sojojin kasar ne za su jagorance ta na wucin gadi

An ayyana tsohon Ministan Tsaron Mali, Ba N’Daou a matsayin shugaban gwamnatin rikon kasar.

Gidan talabijin din Mali ya sanar da haka tare da cewa an nada shugaban gwamnatin sojin kasar, Kanar Assimi Goita a matashin mataimakin Ba N’Daou.

Sanarwar ta ranar Litinin ta ce za a rantsar da shugabannin rikon kasar a ranar Juma’a 25 ga Satumba, 2020 kuma za su jagoranci kasar na watanni kafin a damka kasar a hannun gwamnatin farar hula.

Tun bayan juyin mulkin da sojojin Mali suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar a ranar 18 ga watan Agusta suke fuskantar matsin lamba daga kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) cewa su mika ragamar kasar ga farar hula.

Zuwa yanzu babu tabbacin ko ayyana shugabannin rikon zai kai ga kungiyar ECOWAS ta janye barazanar sanya wa Mali takunkumin tattalin arziki da takatar da ita idan kasar ba ta cika sharudan da kungiyar ta sanya mata ba.