✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sa hannu a fara biyan sabon albashi

Shugaban kasa ya sanya hannun kan dokar biyan N70,000 a matsayin albashi mafi karanci a Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan dokar fara biyan N70,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikata a Najeriya.

A ranar Litinin shugaban kasan ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin albashin a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC), wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran jagoroin bangaren majalisa suka halarta a Fadar Shugaban Kasa.

Halartarsu taron na da nasaba da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a fadin Najeriya daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.

Sanya hannun nasa bisa dokar na zuwa ne kwanaki biyu kafin fara zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa da yunwa a fadin kasar.

Aminiya ta ruwaito yadda a ranar Litinin din, kafin sa hannun shugaban kasan, al’umma a Jihar Neja suka fara zanga-zanga kan halin da kasar ke ciki.

Matasan sun hau kan tituna suna daga kwaleye masu dauke da rubutu da ke nuna bacin ransu kan halin tsadar rayuwa a kasar.

Masu zanga-zangar sun rika rera wakokin nuna adawa da gwamnati a yayin da suke tattaki a kan tituna a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnonin tarayya da na jihohi suna yi yunkuri da dama na don dakatar da zanga-zangar, suna masu cewa zauna-gari-banza da makiya dimokuradiyya za su iya kwace ta.

A makon da ya gabata ne Gwamna Mohammed Bago na Jihar Neja ya ba wa al’ummar jihar da kayayyakin jin kai don hana zanga-zangar.

Ya sanar da biyan alawus din N20,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi.

A cewarsa, “Muna da sama da tan 100,000 na abinci a rumbun ajiyarmu, wanda daga ciki za mu fitar da metrik ton 50,000 a sayar a kan rabin farashin da yake yanzu.

“Kafin karshen shekara, za mu rage farashin kayan abinci da kashi 90 cikin 100, ”in ji shi a wani taro ganawa da al’umma.

Domin nuna jin dadinsu kan kokarin da suke yi na yaki da ’yan fashin daji da sauran miyagun ayyuka, gwamnan ya sanar da bai wa kowane shugaban hukumar tsaro a jihar kyautar Prado Jeep guda daya.

Said dai wa wata sanarwa da ta fitar gwamnatin Neja ta musanta cewa an gudanar da zanga-zanga a jihar.