Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika karin sunayen mutanen da yake son nadawa ministoci ga Majalisar Dattawa.
Tinubu ya aike wa majalisar sunayen ne a yayin da take tsaka da tantance karashen mutane 28 da ya aike mata da farko a ranar Laraba.
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
- Najeriya ta yanke wutar lantarkin da take ba wa Nijar
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya mika sunayen ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio.
A makon jiya ne Tinubu ya mika wa majalisar sunayen rukunin farko na mutanen da yake son nadawa ministoci daga 25 daga cikin jihohi 36 da birnin tarayya da ke kasar — saura sunaye daga jihohi 11.
Jihohin da ake jiran ya mika sunayen ministocinsu su ne: Kano, Legas, Kebbi, Filato, Adamawa, Zamafara, Gombe, Yobe, Edo, Bayelsa, da kuma Osun.
Mutanen da ya fara bayarwa sun hada da mata bakwai da maza 21, wadanda cikinsu kuma akwai tsoffin gwamnoni hudu; ’yan majalisa masu ci uku, tsoffin ‘yan majalisa uku, hadiman shugaban kasa uku, da shugaban hukumar gwamnati daya.
A jerin sunayen da ya bayar da farko, jihohi biyu, Katsina da Kuros Riba sun samu mutum biyu kowannensu.