Ana fargabar mutum daya ya rasu wasu da dama sun samu rauni a turmutsitsin karbar zakkar kudi a Kano a safiyar Laraba.
An samu turmutsutsin ne bayan da mutane suka cika makil a wurin da wani attajirin mai taimakon jama’a ya yi rabon zakkarsa ta shekara-shekara a kusa da barikin sojoji na Bukavu da ke kan titin zuwa Katsina.
Wani ganau da Aminiya ta samu a wurin ya tabbatar mata cewa an fitar da gawar wani wanda ya rasu, a yayin da wakilinmu ya ga an dauko wani daga cikin wurin, wanda ake zargin ya rasu.
Aminiya ta gano cewa mai kamfanin manyan motoci na Nasara Maje, Alhaji Haruna Maje ne ya yi rabon zakkar, inda ake raba wa kowane mabukaci tsabar kudi tsakanin N1,000 zuwa N5000.
- Mutum 27 sun mutu, an jikkata 106 a sabon yakin Libya
- Mu muka harbo jirgin sojin Najeriya —Dogo Giɗe
’Yan sanda da jami’an tsaron Sibil Difensa da aka girke a wurin sun shaida wa wakilinmu cewa ranar Talata aka fara rabon zakkar, ba tare da wata tangarda ba, amma wurin ya rincabe a ranar Laraba, saboda gajen hakurin masu zuwa karba.
“Da farko zun zauna a layi a natse amma sai wasu da ke baya suka fara tasowa zuwa komawa gaba, wanda hakan ya wargaza tsarin da aka yi
“Sannan akwai wasu da suka karba jiya da suka sanar da mutane da yawa, aka zo wurin ya cika fiye da kima.
“Zuwa yanzu, wani gurgu ya rasu, wasu da dama kuma an fito da su daga wurin ranga-ranga, wasu sun ji rauni, wasu kuma sun sume.”
Wasu daga cikin masu karbar zakkar kudin da wakilinmu ya tattauna da su a wurin sun shaida masa cewa a Karamar Hukumar Kumbotso suka ji labarin rabon kudin, suka zo, kuma ba su da ko kudin motar komawa gida.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an tsaro sun dakatar da rabon, inda suka raba ma’aikatan zuwa ofishin kamfanin.
Kafin nan, attajirin ya bar wurin, saboda yadda al’amuran suka rincabe. Kokarin wakilinmu na yi magana da manaja ko ma’aikatan kamfanin ya ci tura, saboda duk sun ki yin bayani.
“Kamar yadda kake ganin, mun dakatar da rabon sai abin da hali ya yi, da farko komai na tafiya cikin tsari, kafin daga baya mutane su wargaza komai,” in ji daya daga cikinsu da ya nemi a boye sunansa.
Masu son karbar sadakar kuma sun ki watsewa daga wurin duk da cewa an dakatar.