✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 27 sun mutu, an jikkata 106 a sabon yakin Libya

An kashe akalla mutum 27 an jikkata wasu 106 a sabon yakin da ya barke a kasar Libya.

Akalla mutum 27 ne aka kashe tare da jikkata wasu akalla 106 a kazamin yakin da ya barke a kasar Libya.

A safiyar Laraba jami’an lafiya suka sanar da alkaluman a sakamakon sabon yakin da ya barke a tsakanin wasu manyan kungiyoyin mayakan sa-kai masu gaba da juna a birnin Tripoli.

Cibiyar kula da lafiya ta gaggawa da ke birnin ne ya fitar da alkaluman na wucin-gadi kafin wayewar gari ta shafinta na Facebook.

Kazamin fadan ya barke ne tsakanin mayakan sa-kai na 444 Brigade da kuma Al-Radaa, da ke kokarin karbe ikon birnin tun bayan tun bayan juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban kasar, Muammar Kadhafi a shekarar 2011.

A ranar Litinin ne sabon yakin ya barke, aka ci gaba da shi har zuwa washegari.

Akalla iyalai 234 ne aka kwashe daga wuraren da ake gwabza fadan tare da jami’an lafiya da suka makale a yayin da suke kula da wadanda aka jikkata.

An kafa cibiyoyin lafiya uku tare da motocin daukar marasa lafiya 60 a yankunan da sabon yakin ya barke.

Sabon fadan ya samo asali ne bayan tsare jagoran mayakan 444 Brigade, Kanar Mahmud Hamza, da mayakan Al-Radaa Force suka yi ranar Litinin.

A ranar Talata majalisar yankin Soug el-Joumaa, cibiyar Al-Radaa Force, ta sanar cewa an cimma yarjejeniya da Fira Minista Abdelhamid Dbeibah, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta aminta da shi, cewa za mika Hamza ga bangaren ’yan ba ruwanmu.

Majalisar ta kuma sanar cewa za a tsagaita wuta bayan an mika shi, inda a cikin daren Talata fadan ya yi sauki.

Bangororin biyu na tare da gwamnatin Dbeibah da ke neman ikon kasar ta hanyar kawance da mayakan sa-kai.