’Yan Najeriya a kafafen sada zumunta, musamman Facebook da X da TikTok wanda sun sha ce-ce-ku-ce tsakaninsu da ’yan wasu ƙasashe irin su Ghana, Afirka ta Kudu da Nijar a 2024.
Ga wasu daga cikin dambarwar:
Najeriya da Ghana:
Kallon hadarin kaji tsakanin Najeriya da ’yan Ghana abu ne da ya saba faruwa musamman idan ana maganar abubuwan more rayuwa da ci-gaban ƙasa. ’Yan Najeriya na ganin cewa sun fi ’yan Ghana ta ɓangarori da dama, su ma ’yan Ghana na ganin sun yi wa Najeriya fintikau ta ɓangaren ci-gaba musamman abin da ya shafi wutar lantarki, fasaha da sauransu.
’Yan Najeriya na ganin duk da cewa Ghana ta fi su tsayayyiyar wutar lantarki, amma daga ƙasarsu Ghanan ke samun kaso mafi yawa na wutar da take tinƙaho da shi, don haka ’yan Ghana ba su da dalilin jin cewa ƙasarsu ta fi Najeriya wuta duk da cewa sun yarda cewa kamfanonin rarraba raba wutar lantarki a ƙasarsu sun gaza wajen samar da ita a wadace a cikin gida.
A shekarar 2024 Najeriya ta yi fama da matsalar ɗaukewar wuta gaba ɗaya, bayan katsewar babba layin lantarkin ƙasarta fiye da sau bakwai. Wannan ya sa mutan Ghana tabbatar da cewa lallai sun fi Najeriya tsayayyar wutar, lamarin da ya janyo zazzafar muhawara.
Najeriya da Libya:
A shekarar ta 2024, ’yan Najeriya da Libya sun zargi juna kan wasannin neman gurbi shiga Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) na shekarar 2025. Hukumomi a Najeriya sun yi zargin cewa Libya ta tsare tawagar ’yan wasan Super Eagles a daya daga cikin filayen jiragen kasar gabanin wasan ƙasashen biyu.
Tawagar ’yan wasan Super Eagles na Najeriya sun maƙale a filin jirgin saman Al Abraq bayan saukarsu a ƙasar Libya domin fafatawa. Rahotanni sun bayyana cewa masu masaukin baƙi ne suka karkatar da jirgin ’yan Najeriya daga sauka a birnin Benghazi zuwa Al Abraq.
Bayan haka, suka toshe wa ’yan Najeriyar duk wasu hanyoyin shiga da fita da kuma sadarwa sama da awa 10 a filin jirgin, zargin da hukumar kasar Libya ta musanta, duk da cewa ta amsa cewa matsala ce ta auku kamar yadda suma lokacin da ’yan wasansu suka sauka a Najeriya suka fuskanci yanayi irin wannan, har ’yan kasar suka jima a filin jirigin da suka sauka kafin daga bi sani a yi safararsu zuwa jihar da aka buga wasa a motoci.
Wannan lamari ya ja ce-ce-ku-ce matuka tsakanin bangarorin biyu, kuma an tafka muhawara mai zafi kafin daga baya kura ta lafa.
Najeriya da Afirka ta Kudu:
’Yan Najeriya a kafofin sada zumunta sun ja zare da ’yan Afirka ta Kudu, bayan cire Chidinma Adetshina, daliba da ke karanatar ilmin shari’a a kasar daga shiga gasar Sarauniyar kyau da aka yi, kan zargin cewa mahaifinta dan Najeriya ne duk da cewa ita haifaffiyar birnin Johannesburg ce.
Wannan lamari ya dugunzuma ’yan Najeriya, kuma sun yi kakkausan martani ga ’yan Afirka ta Kudu, inda suka zarge su da nuna kabilanci.
A kafafen sada zumunta da dama sun caccaki juna wanda har kai ga wasu ’yan Najeriya bayyana rashin jin dadinsu da kuma yunkurin daina hulda da ’yan kasar a matsayin hanya mafi sauki na nuna masu fushinsu.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan ya sa wasu ’yan Afirka ta Kudu suka rika kiran direbobin Bolt na Najeriya da zummar su kai su wani wuri, sai sun je wurin su ga wayam, sai su turo masu sakon cewa da wasa suke yi su ’yan Afirka ta Kudu ne kuma suna kasarsu.
Daga bisani ’yan Najeriya suka mayar da maratani inda suka rika gomman kiran motocin bolt zuwa wuri guda, da kuma odar kayayyaki daga shagunan zamani zuwa gidajen ’yan Afirka ta Kudu, lamarin da sai ta ta kai ga ’yan direbobin bolt din kasar suka rika nuna takaicinsu da irin asarar da suke yi na mai.
A karshe sai da Bolt ta soke tsarin yin odar hayar motoci daga kasar waje a Afirka ta Kudu.