Babbar Kotun Jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, daga jam’iyyar.
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako ta kuma haramta wa Ganduje bayyana kansa a matsayin dan Jam’iyyar APC.
Umarnin kotun ya kuma hana Ganduje shugabantar duk wata mu’amala da ta danganci jam’iyyar.
Mai Shari’a Naabba ya bayar da wannan umarni ne sakamakon neman hakan da Barista Dokta Ibrahim Sa’ad ya yi a madadin shugabannin APC na mazabar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa.
Shugabannin sun hada da Sakataren Jam’iyyar, Laminu Sani da Haladu Gwanjo, wadanda suke cikin shugabannin mazabar tara da suka dakatar da Ganduje.
An dai dakatar da tsohon gwamnan Kano, Ganduje, daga Jam’iyyar APC ne a mazabarsa, kan zargin rashawa.
A ranar Litinin ne dai shugabancin jam’iyyar na mazabar Ganduje suka sanar da dakatar da shi.
Amma daga bisani wani sashi na shugabancin jam’iyyar an kuma na jiha ya sanar da korar wadanda suka sanar da dakatar da Gandujen.
Kotun dai ta dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.
Wannan dai na zuwa ne a ranar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ke sa ran gufanar da Ganduje da gaban kuliya kan zargin almundahana a zamanin mulkinsa a jihar.