✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Neja ya kamu da coronavirus

Gwamnan Jihar Niger Abubakar Bello ya sanar da cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Gwamnan Jihar Niger Abubakar Bello ya kamu da cutar coronavirus.

Gwamna Abubakar Bello ya bayya na haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba, 2020.

“Na kamu da cutar OVID-19 kuma na killace kai na”, inji shi.

Kamuwar gwamnan da cutar na zuwa ne a daidai lokacin da mahukunta lafiya a Najeriya ke gargadin cewa akwai yiwuwar ta sake dawowa da tsanani bayan saukinta da aka samu.

A ranar Litinin kuma hukumomin lafiya a duniya na bayyana kwarin gwiwa game da maganin cutar coronavirus da kamfanin Pfizer ya zamar wanda ake ganin da shi haka za ta cimma ruwa.

Kawo yanzu rahotannin masana lafiya na cewa kashi 90 na maganin rigakafin na kamfanin Pfizer da aka yi gwaji ya yi nasara, kuma babu alamar ya yi wata illa ga mutanen da aka yi wa amfani da shi.