✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Edo ya fice daga APC bayan ganawa da Buhari

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki bayan ya gana da Shugaba Buhari. Matakin ya biyo bayan hukuncin…

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki bayan ya gana da Shugaba Buhari.

Matakin ya biyo bayan hukuncin da Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Gwamna na jam’iyyar a jiharsa ya yanke na hana shi takara a cikinta saboda zargin rashin sahihancin takardunsa.

Obaseki ya sanar da ‘yan jaridar Fadar Shugaban Kasa ficewarsa daga APC a ranar Talata, sannan ya karyata zargin da ake masa na amfani da takardun bogi.

Gwamnan dai ya ziyarci fadar ne inda ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun haramta masa shiga zaben fid da gwanin jam’iyyar da aka yi ranar Juma’a.

Tun da farko jam’iyyar ta ce ta yanke hukuncin hana shi damar yin takarar ne sakamakon shakkun da take da shi kan ingancin takardunsa.

Tuni dai jam’iyyar PDP ta ce a shirye take ta karbe shi in zai dawo cikinta, amma ba za ta yi masa alkawarin tikitin takara kai tsaye ba don shiga zaben gwamnan jihar karo na biyu.

An dai yi ta samun takun saka tsakanin gwamnan da tsohon mai gidansa, kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa mai ci, Adams Oshiomhole kan batun sake tsayawarsa takara da ma wasu batutuwan.

Rikicin nasu dai ya yi sanadiyyar darewar jam’iyyar a jihar ta Edo zuwa gida biyu.

Tsagin da ke biyayya ga bangaren Oshiomholen dai ya amince da Fasto Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takararsa a zaben fid da gwanin da za a yi ranar 22 ga watan Yuni.

Ko a cikin makon nan dai sai da Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar a matakin kasa ya yi yunkurin sasanta bangarorin biyu amma hakarsa ta gaza cimma ruwa.