Mayaka da ake zargi ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare a kananan hukumomi biyu a jihar Borno.
Mazauna sun ce maharan sun shigo garuruwan da safiyar Asabar, suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi da nufin kwace ikon garuruwan.
Wani ma’aikacin agaji ya shaida wa wakilin Aminiya cewa yanzu rugugin fashewan abubuwa da harbe-harbe sun cika ko’ina a garin Monguno.
Ya ce sojoji sun isa garin inda bangarorin biyu ke ta musayar wuta a garin da ke Karamar Hukumar Monguno.
“Yanzu haka ‘yan Boko Haram sun kawo wa Monguno hari. Karar harbi da fashewan abubuwa muke ji, amma sojoji na kokarin kora su. Muna cikin hadari, don Allah ku sa mu a addu’a.”
A safiyar ce kuma, mayakan kungiyar suka kai hari a garin Usmanti Goni da ke Karamar Hukumar Nganzai.
Maharba a garin sun ce da zuwan mayakan na Boko Haram din sai suka yi ta bude wuta a kan farar hula.
Sun kara da cewa ba a san adadin wadanda ‘yan Boko Haram din kashe ko suka samu rauni ba.
Amma sun ce a nan din ma sojoji sia kuma suna ci gaba da artabu da ‘yan kungiyar.
A makon da ya wuce ne wasu ‘yan Boko Haram suka kai hare-haren da suka kashe fararen hula 81 da daruruwan dabbobi a Karamar Hukuman Gubio a jihar ta Borno.
Maharan sun kuma yi garkuwa da hakimin Gubio da wasu mutum 6 sannan suka sace daruruwan dabbobi.