Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dakatar da Gwamna Godwin Obaseki na Edo daga shiga zabenta na fitar da dan takararta a zaben gwamnan jihar da ke tafe.
Jam’iyyar ta ce ta yi hakan ne saboda samun bayanai masu karo da juna game da sakamakon Mista Obaseki na jarrabawa.
Kwamitin tantance ‘yan takarar da shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole ya kafa ranar Laraba don duba cancantar mutum shida da ke sha’awar tsayawa ne dai ya yanke hukuncin dakatar da Obaseki.
Baya ga gwamnan, kwamitin ya haramta wa wasu mutane biyu shiga zaben na fitar da gwani.
An dai jima ana takun saka tsakanin Gwamna Obaseki da wanda ya gada a kan kujerar, Shugaban Jam’iyya Adams Oshiomhole, lamarin da ya raba kan ‘ya’ayan jam’iyyar ta APC reshen jihar Edo.
Rarrabuwar kawuna
Magoya bayan Mista Oshiomhole dai sun riga sun ayyana Pastor Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takararsu.
Tuni dai gwamnan ya mayar da martani yana cewa ba zai daukaka kara a kan hukuncin na “rashin adalcin” ba.
Da ma dai gwamnan ya koka cewa matukar Mista Oshiomhole yana da hannu a aikin tantance masu son tsayawa takarar, to ba za a yi masa adalci ba.
“Tun da Kwamared Adams Oshiomhole yana da manufa a wannan lamari, ba na zaton za a yi min adalci yayin tantancewar, amma dai za mu jira mu ga yadda za ta kaya”, inji gwamnan.