A cikin jawabinsa ga ’yan kasa a lokuta daban-daban a zaman zagayowar Ranar Demokuradiyya ta bana da kuma kasancewarsa shekara guda a kan karagar mulkin kasar nan a inuwar jam`iyyarsu ta APC, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta sake nanata irin yadda ya samu kasar nan a cikin mawuyacin halin kama daga batun tattalin arzikin kasa da na tsaro da cin hanci da rashawa da suka yi katutu a cikin kasa baki daya, baya ga karya doka da oda da suka zama tamfar jini da tsoka ga akasarin ’yan kasar nan, amma dai duk da haka, shugaban ya sha alwashin gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen ganin ta shawo kan irin wadannan matsaloli.
Shugaba Buhari ya fadi cewa duk da irin dimbin kudaden da kasar nan ta samu a kan arzikin man fetur, amma ya yi mamaki kuma ya kadu matuka da ya zo kan karagar mulki, ya fahimci ba kudaden ba kuma abin da aka yi da su a kasa, ko don tanadin kauce wa irin wannan mawuyacin hali da yanzu kasar da al`ummarta suka shiga.
Tabbas koda mutum bai san irin barnar tallalin arzikin da mahukuntan da suka jagoranci mulkin demokuradiyyarmu na tsawon shekaru 16, kafin zuwan Gwamnatin Shugaba Buhari ta jam`iyyar APC, suka yi ba, amma dai ya san irin zaman zullumin da aka shiga kasar nan a sanadiyar gwagwarmayar ’yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-da’await Wal-Jihad da aka fi sa ni da Boko Haram, bisa ga yadda su ka hana kasar nan sak, musamman a Borno da Yobe da Adamawa da Gwambe, jihohin da suke cikin shiyyar Arewa maso gabas da wasu sassan kasar nan. Rikicin da har ya samu tsallakawa cikin kasashen makwabtanmu irinsu Janhuriyar Nijar da ta Benin da Kamaru da Chadi. Amma Allah cikin ikonSa a cikin shekara dayar nan ta mulkin Buhari, wannan gwagwarmaya da aka fara tun a shekarar 2009, tana kokarin ta zama tarihi, bisa ga jajircewa da Gwamnatin Buharin ta yi, na kawo karshe rikicin.
Haka ma batun yake a kan yaki da cin hanci da rashawa, bayan da hukumomin da batun ya rataya a wuyansu irinsu EFCC da ICPC da CCT da sauran hukumomi, sun farka daga magagin barcin da ya dauke su, tun a zamanin Gwamnatin PDP ta tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, yanzu suna aiki ba dare ba rana, musamman a kan rahotannin binciken hukumomin na EFCC da takwarorinta, a kan fallasar yadda tsohon mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) da tsohuwar Ministar albarkatun man fetur uwargida Diezani Alison Madukue, suka rarraba biliyoyin Nairori na sawo makamai da na cinikin man fetur ga wasu masu fada a ji na kasar nan, da zummar ko ana ha-maza ha-mata, sai Shugaba Jonatahan ya koma kan karagar mulki a babban zaben na bara.
Zuwa yanzu dai kowa ya gani ya kuma shaida cewa yakin kwato dukiyar da irin wadancan mutane su ka wawure da gaske ake, kuma ba wasu shafaffu da maid a za a kyale sai dai in bincike bai zo kansu ba, kamar yadda shugaban Hukumar EFCC Alhaji Ibrahim Magu da shugaba Buhari su ka sha nanatawa, kodayakeshugaba Buhari bai cikasawa ’yan kasa alkawarin da ya yi ba na cewa a bikin ranar zai bayyanawa ’yan kasa jerin sunayen wadanda suka tsiyata kasar nan da yawan dukiyar da su ka sace,amma sai ga shi a jawabin nasa ya sa giyar ribas, ya ce Ma`aikatar yada labarai ita za ta bayyana irin wadancan mutane bayan tabbatar da kammala cikakken bincike ta hanuyar da doka da oda suka tanadar.
Yanzu kuma babban yakin da ya kamata Gwamnatin Shugaba Buharin ta maida hankali, ’yan kasa kuma su goya ma ta baya, shi ne na yadda za ta rage irin yawan kudaden da ake wa musamman zababbun kasar nan hidima, tun daga sama har kasa. Abin da ya sanya na ce haka bai wuce tunda aka fara wannan mulkin demokuradiiya bisa ga tsarin shugaba mai cikakken iko irin na kasar Amurka, masana tattalin arzikin kasa suke ta kiraye-kirayen lallai sai a duba wannan tsari domin ya yi matukar tsada, da hasashen cewa nan gaba ba za mu iya daukar nauyin tafiyar da shi ba. Allah cikin ikonSa ga lokacin ya zo, da har ta kai yanzu ana maganar jihohi 27, daga cikin 36, na kasar nan ba su iya biyan albashin ma`aikatansu, bare su yi wa mutanensu ayyukan raya kasar da suka yi masu alkawurra. Wannan karayar arziki ta sa zuwa yanzu ta Babban Bankin kasar nan, Gwamnatin Tarayya ta ba irin wadancan jihohi lamunin N358 biliyan, daga cikin N662 biliyan da suka nema, amma dai har yanzu mafi yawan jihohin na ruwa a kan kasa bliyan albashin.
A bisa ga wannan yanani na mawuyacin halin karayar tattalin arzikin kasa, ya sanya nake ganin yanzu ne ya kamata Gwamnatin Tarayya ta duba irin yawan makudan kudaden albashi da alawus-alawus da ake biyan ’yan Majalisun Dokoki kama daga na tarayya zuwa na jihohi, ’yan majalisun da tun kafin a shiga wannan hali masana fannin tattalin arzikin kasa da na siyasa, su kai ta kiraye-kirayen lalle gwamnati ta san na yi domin a fahimtarsu tsarin ya yi matukar tsada. To, yanzu tsadar ta bayyana karara, amma su daga wajensu babu alamun suna jin matsin rayuwar.
Don kuwa labarin da jaridar Daily Trust ta ranar 24 ga watan Mayun da ya gabata ta kalato daga Hukumar rarraba arzikin kasar nan (RMAFC), ya tabbatar da hakan. Alal misali, a cikin wancan rahoton, jaridar ta tabbatar da ana kashe sama da N6 biliyan duk shekara, kimanin N6 miliyan a kan kowane dan Majalisar Dokoki na jihohin kasar 36, da adadinsu ya kai 978, a zaman albashi da alawus-alawus. Bayan albashin N1.34 miliyan duk shekaru, sannan akwai N2 miliyan, na alawus din kawata gida, duk bayan shekaru hudu, baya ga bashin sayen abun hawa na N5.3 miliyan, biya cikin shekaru hudu. In takaice ma mai karatu labara, ’yan majalisun suna da alawus-alawus na kudade masu ciwo har iri 12. Dadin-dadawa kuma ga shi kamar yadda ta bayyana yanzu gwamnatocin jihohinsu na sai masu motocin alfarma, bayan rancen sayen ababen hawan da suka ba su.
Ko su ma ’yan Majalisun Dokoki na kasa Sanatoci da Wakilai, zuwa yanzu ta bayyana Majalisar Dattawa ta fara karbar jerin motoci 36, daga cikin 108, da ta shirya sai ma kowane Sanata a kan kudi N36.5 miliyan, kudaden da za su ta shi akan N3.8 biliyan. Su kuma na Majalisar Wakilai kowane Fijo kirar 508, aka saya masa a kan N10 miliyan, kudaden da suka kama a kan N3.6 biliyan.
Lalle kam, bisa ga irin halin da tattalin arzikin kasar nan ya samu kansa daga faduwar farashin man fetur, yanzu ne Hukumar rarraba arzikin kasar ya kamata ta waiwayi albashin su Honorabul, ko dai ta rage shi da akalla kashi 50 cikin 100, wato rabi ke nan, ko kuma ’yan kasa su fara shirin yadda za a gyara tsarin mulkin kasar nan da zai maida ayyukan ’yan majalisar ya zaman wucin gaji, ba na dindindin ba kamar yadda ya ke yanzu.
Yanzu ya kamata a rage bukatun zababbu da nadaddu
A cikin jawabinsa ga ’yan kasa a lokuta daban-daban a zaman zagayowar Ranar Demokuradiyya ta bana da kuma kasancewarsa shekara guda a kan karagar mulkin…