Hukumar gudanarwar kulob din Spotlight da ke Katsina ta ba sanarwar zaftare rabin albashin ’yan kwallonta da kuma koci Abdullahi Heyman. Hukumar ta ce ta yi haka ne saboda yadda kulob din Kwara United ya lallasa na Sportlight a gasar rukunin ’yan dagaji a karshen makon jiya da ci 5-0.
Mai kula da yadda al’amurra ke gudana a kulob din Alhaji Ayuba Umar ne ya bayyana haka a lokacin da yake hira da manema labarai. Ya ce gewamnatin Jihar Katsina ta yanke shawarar daukar wannan mataki ne don nuna bacin ranta ga koci da kuma daukacin ’yan kwallon na rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana duk da makudan kudin da gwmanati ke kashe musu. Ya ce daga yanzu ’yan kwallon da kocin ba za su rika samun cikakken albashi ba har sai sun cigaba da nuna kwazo a sauran wasanninsu.
Ya ce duk da tagomashin da gwamnatin Jihar Katsina take yi wa ’yan kwallon amma abin mamaki sai ga shi sun kasa ba marada kunya.
“Babu dan kwallo ko koci da ke bin mu bashin ko kwabo, hasalima tuni aka biya su albashin watan Afrilun da ya gabata don haka babu dalilin da zai sa su rika kunyata mu a fagen kwallo”, inji shi.
Ya ce baya ga zaftare albashinsu, an kuma aika takardar gargadi ga koci Abdullahi Heyman don ganin ya zage damtse a sauran wasannin da suka rage.
Yanzu rabin albashi ake ba ‘yan kwallon Spotlight na Katsina
Hukumar gudanarwar kulob din Spotlight da ke Katsina ta ba sanarwar zaftare rabin albashin ’yan kwallonta da kuma koci Abdullahi Heyman. Hukumar ta ce ta…