Zuwa yanzu tsohon Sakataren yada labarai na jam`iyyar PDP na kasa baki daya Mista Olisa Metuh, ya sha alwashin mayar da tsabar kudin nan Naira miliyan arbaminya (N400miliyan), ga Hukumar yaki da ta`annati da kudin jama`a ta EFCC. Wadannan kudi na cikin kudin nan Dalar Amurka biliyan 2.2 ($2.2 biliyan), wadanda a rubuce Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ta ce ta ware don sawo makamai, don tunkarar masu tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, inda ake fama da rikicin ’yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Da`awati Wal jihad da aka fi sani da Boko Haram da ake ta fama su tun a shekarar 2010, musamman a jihohi irin su Borno da Yobe da Adamawa da Gwambe, rikicin da ya haddasa asarar rayukan dubun-dubatar wadanda suka rasa rayukansu da wadanda aka jikkata, baya ga sama da miliyan uku da suka zama `yan gudun hijira a cikin kasar nan da kasashe da ke makwabtaka da mu, ba a ma batun dukiya da kaddarorin da aka lalata. Kudin da yanzu ta bayyana an karkatasu a kan yakin neman a sake zaben Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a shekarar 2015.
Aniyar Mista Metuh na ya shirya zai mayar da wadancan makudan kudi na cikin jawabin da lauyansa Babban lauyan kasa Onyechi Ikpeazu, ya fitar a ranar Alhamis din makon jiya a Abuja, inda ya ce Mista Metum zai yi haka ne a zaman ta sa gudummuwar a kan yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta APC ta dukufa a kai. Dadin dadawa lauyan ya ce yin hakan ya nuna a fili irin kyakyawar aniya da mutunci da gaskiyar shi Mista Metuh a cikin wannan batu na yaki da cin hanci da rashawa na wannan gwamnatin.
Babban lauyan, wanda kuma yake kare Mista Metuh da Kamfaninsa na zuba jari mai suna Destra Inbestments a kan gurfanarwar da Hukumar ta EFCC ta yi musu gaban wani babban kotun tarayya da ke Abuja a cikin watan Janairun bana a kan zargin sun karbi wadancan makudan kudi daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, a wani lokaci cikin watan Disambar 2014, ya ce lokacin da a ka ba wanda yake karewa din wadancan kudi, ba shi da masaniyar daga inda kudi suka fito. Ya ce sai yanzu ne daga jawaban mai gabatar da kara da kuma na shaidunsu ya fahimci haka.
Ya ci gaba da cewa, lokacin da batun binciken kudin ya taso, a ka kuma gayyaci wanda ake tuhumar a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro a cikin watan Disambar bara, Mista Metuh ya nemi sanin inda kudin da aka ba shin suka fito. Aka kuma sanar da shi cewa daga aljihun gwamnatiun tarayya suka fito. Wai in ji lauyan nasa tun daga wancan lokaci Mista Metuh ya dauki alkawarin zai biya kudin har Naira miliyan 400, tunda daga lalitar gwamnatin tarayya aka dauko su.
Kai ka ji mai karatu, Bahaushe na karin maganar cewa “Idan mai fadin magana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne.” Alhali Mista Metuh nan ne a zamansa na Kakakin jam`iyyarsa ta PDP, kafin daga bayan kama shi da Hukumar EFCC din ta yi yake ta babatun cewa zarge-zargen da ake yi masa da wasu mukarraban gwamnatin jam`iyyarsu ta PDP na yin watanda da wadancan makudan kudi ba komai ba ne illa zargi marar tushe da kuma neman a bata wa mutane masu mutunci irin su suna.
Alal misali a zaman nuna turjiya da musanta zargin da ake yi masa na karbar wadancan makudan kudin makamai, har sai da ta kai lokacin da Hukumar EFCC cikin tana binciken Mista Metuh kafin ta gurfanar da shi gaban kuliya, ta kai fagen da hukumar ta EFCC, ta fitar da sanarwar cewa Mita Metuh ya yi barazanar zai daina cin abinci, da a ce dai ya biya kudin da bai san da su ba.Mai karatu barazanar yajin kin cin abinci, wata barazana ce da `yan gwagwarmaya ko wadanda suka kware wajen aikata ta`asa a duniya suke amfani da ita wajen janyo hankalin kasashe da kungiyoyin duniya kan halin da suke ciki na tuhuma, tamfar kuntatawa da cin zali ne mahunkuntar kasashen su ke yi musu, da suke neman daukin irin wadancan kasashe da kungiyoyi.
Kodayake an ce iyalan Mista Metuh, sun taka rawa wajen ganin sun tilasta wa dan uwansu lallai ya biya wadancan kudi, rawar da ba dalilin da zai sanya su taka ta muddin ba su da tabbacin cewa dan uwansu ya ci wadancan kudi, don kuwa Naira miliyan 400, ba kwabo 40 ba ne, a irin wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arzikin kasa. Dadin-dadawa, Mista Metuh da `yan uwansa da ma lauyansa yanzu duk suna sa ran cewa idan har ya biya kudin, Hukumar EFCC za ta janye tuhumar da take yi masa, don ya huta da irin terere da jeka-ka-dawo da ake da shi a gaban kuliya. Al`amarin da ko kusa bai kamata ba, kamata ya yi duk wanda aka samu da laifin sama da fadi da dukiyar mutanen kasar nan, to lallai ya kamata bayan an tilasta shi ya biya, to, kuma a gurfanar da shi gaban kuliya don ya girbi abin da ya shuka, kuma hakan ya zama izina ga sauran `yan kasa. Ta haka kawai kasar nan za ta samu alkibla madaidaiciya a kan zalunci da cutar da aka dade ana yi wa talakawan kasa.
Mai yiwuwa Mista Metuh ya dauka wannan gwamnatin ta APC, tamfar gwamnatinsu ce ta PDP, mai fada ba cikawa a kan makomar kasar nan, musamman wannan babban yaki na cin hanci da rashawa da shi ne ummulhaba`isin da ya tsugurnar da kasar nan. kila jin irin kular da ya shiga a cikin `yan watannin nan, ya gane cewa shayi ba ruwa ba ne. Lallai hukumomi irin su EFCC ya kamata su kara baza kaiminsu wajen wannan gagarumin yaki da azzaluman kasar nan. A nan kuma lallai Gwamnatin Ttarayya da mukarrabanta manya da kanana da sauran `yan kasa su kama wa hukumomi irin na EFCC, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu, ko a samu fitar da kasar nan daga rukuki, har ta samu kai ga gaci.
BARKA DA SALLAH
Wanna fili yana yi wa dubun dubatar miliyoyin Musulmin duniya Barka da Sallah da fatan dukkan ibadun da muka gabatar su zama karbabbu wajen Allah SWT. Allah Ya sa mu dora a kan irin darussan da muka koya a cikin watan azumin na gudanar da ibadu da yawaita kyauta da sadaka da kyautatawa, tare da tausaya wa junanmu da yin dukkan ayyukan da za su kara kusantar da mu ga Allah da ManzonSa. Allah Ya zaunar da mu lafiya Ya bai wa shugabanninmu karfin imanin yadda za su tafiyar da mulkinmu cikin gaskiya da adalci, amin summa amin. Allah Ya maimaita mana amin summa amin.
Yanzu Metuh ya san shayi ba ruwa ba ne
Zuwa yanzu tsohon Sakataren yada labarai na jam`iyyar PDP na kasa baki daya Mista Olisa Metuh, ya sha alwashin mayar da tsabar kudin nan Naira…