✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yanzu garau nake, inji Tinubu bayan jinyar wata uku a Birtaniya

Tinubu ya shafe wata uku a Birtaniya yana jinyar gwiwarsa da aka yi wa tiyata.

Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya ce yanzu yana jin jikinsa garau, ba tare da wata matsala ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan dawowarsa daga Birtaniya inda ya yi wata uku yana jinyar gwiwarsa.

  1. Ziyartar Tinubu: Yadda su Wammako suka kashe N265m
  2. Ya sayar da kodarsa ya sayi wayar iPhone, daya kodar kuma ta daina aiki

“A lokacin da yake kasar wajen an yi masa tiyata a gwiwarsa ta dama tare da gashi; Babu wata tiyata kuma da aka yi masa ko yake son a yi masa a nan gaba, sabanin ji-ta-ji-ta da aka yi ta bazawa,” inji sanarwar da hadiminsa ya fitar.

Tinubu wanda ya ce zai ci gaba da aiki domin wanzar da shugabanci a Najeriya, ya sa an soke wani gagarumin bikin tarbar sa da jam’iyyarsa ta APC ta shirya gudanarwa a ranar Lahadi.

Ana hasashen cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas din, kuma mai fada a ji jam’iyyar APC, musamman a yankin Kudu maso Yamma, yana shirye-shiyen fitowa neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

A yayin da yake waje, Shugaba Buhari da gwamnoni ’yan majalisar tarayya da manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa sun yi ta tururuwar zuba duba shi, lamarin da ya haifar da zargin kashe kudaden gwamnati.