Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubaka, ya buƙaci a bai wa Sarakunan Gargajiya kariya a matsayin wani ɓangare na tsarin mulki a Najeriya.
Rikicin masarautar Kano da jita-jitar yunƙurin tsige Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III a Jihar Sakkwato sun tayar ƙura a ƙasar.
- DAGA LARABA: Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro
- Albashi: Gwamnoni za su yi taron gaggawa
Atiku, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce dole ne a kare masarautun gargajiya daga gwamnatocin jihohi.
“Abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan a ƙasar nan sun nuna yadda gwamnatocin jihohi ke amfani da ƙarfinsu kan sha’anin masarautun gargajiya. Lamari ne da ya shafe mu ta kowace fuska,” inji shi.
“Saboda haka, dole ne a kare masarautun gargajiya daga rikici a tsakaninsu da gwamnatocin jihohin da ke barazana ga zaman lafiyarsu. Idan mulkin sarakunan gargajiya ya kasance babu kwanciyar hankali, zai yi wuya a samu zaman lafiya a tsakanin al’umma.
“Ko da yake kundin tsarin mulkinmu, bai yi tanadi ga masarautun gargajiya ba, abubuwan da muka samu sun nuna ƙarara cewa suna taka rawar gani game da tattalin arziƙin yankunansu, da kuma samar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.
“Ina so na tunatar da cewar, masarautun gargajiya sun kafa tsarin mulki kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Kuma sun yi mulki da tsari. Saboda haka, dole ne a ba su kariyar da ta dace.
“Saboda haka, ina kira a sauya fasalin kundin tsarin mulkinmu ta yadda zai amince da masarautun gargajiya ta hanyar fayyace ayyukansu da ofisoshinsu. Wannan gyara na da muhimmanci idan aka yi la’akari da yunƙurin da suke yi wajen daƙile ayyukan ta’addanci.
“A ƙarshe, dole ne na yi kira ga gwamnonin jihohi da suke girmama sarakunan gargajiya. Al’adun da sarakunanmu na gargajiya ke wakilta su ne jimillar gadonmu a matsayinmu na jama’a.”