Mahalarta ɗaurin aure mutum 19 daga Jihar Kano sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota a yankin Kwanar Maciji da ke Ƙaramar Hukumar Pankshin a Jihar Filato.
Mutum 11 daga cikinsu sun tsallaka rijiya da baya da raunuka a haɗarin da ya ritsa da su a yayin da suke hanyar komawa gida bayan ɗaurin auren da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a ranar Asabar.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Pankshin, John Dasar, ya bayyana cewa motar matafiyan ta kama da wuta ne, amma an yi nasarar ceto direban da wasu fasinjoji.
Ya ce, “an ceto mutane 11 amma mutane 19 sun kone ƙurmus ba za a iya gane su ba, saboda bayan mutane sun zo ana ƙoƙarin ceto fasinjojin ne motar ta kama da wuta, ta cinye ragowar.”
Ya ce an kai waɗanda suka tsira Babban Asibitin Pankshin inda ake duba lafiyarsu.