✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan wasan Premier biyu sun kamu da coronavirus

Hukumar da ke kula da gasar Premier ta Ingila ta bayyana a ranar Asabar cewa an samu ‘yan wasa biyu da suka harbu da cutar…

Hukumar da ke kula da gasar Premier ta Ingila ta bayyana a ranar Asabar cewa an samu ‘yan wasa biyu da suka harbu da cutar coronavirus a kashi na biyu na gwaje-gwajen da ake gudanarwa akan ‘yan wasa.

Tun bayan dawowar atisaye cikin kananan rukuni da ‘yan wasa sukayi a ranar Talata, gwaje-gwajen da aka gudanar sun nuna ‘yan wasa takwas sun harbu da cutar.

A wani sako da hukumar kula da gasar ta fitar da ke tabbatar da hakan tace.

“Premier a yau (Asabar) ta tabbatar da cewa a ranakun Talata, Alhamis da Juma’a, an gudanar da gwaje-gwaje akan ‘yan wasa da sauran ma’aikata 996 wanda a cikin su aka samu mutane biyu da suka harbu daga kungiyoyi daban-daban.

‘Yan wasa da ma ma’aikatan da aka tabbatar sun harbu da cutar za su killace kansu na tsawon kwanaki bakwai” in ji hukumar.

Bugu da kari hukumar ta ce ba za ta bada bayanan mutane biyun da suka harbu da cutar ba.

An gudanar da gwaje-gwaje a kan mutum  748 a kashin farko a ranakun Lahadi da Litinin wanda a cikin su ne aka samu dan wasan kungiyar Watford, Adrian Mariappa da wasu ma’aikatan kungiyar biyu da suka harbu.

Ya zuwa yanzu dai sun killace kan su zuwa tsawon kwanaki bakwai.