A farkon Gasar Euro ta bana mun hadu a Bakin Raga inda muka tattauna sannan muka yi hasashen kasashen da za su iya lashe gasar.
Daga cikin kasashen da muka yi hasashen akwai Ingila da Italiya, sai ga shi su biyun kuma sun kai wasan karshe.
Hakan ya sa muka sake komawa Bakin Ragar domin tattaunawa game da wasan na karshe.
Salisu Musa Jegus ya ce yana hasashen Ingila za ta lashe gasar domin, a cewarsa, “Na farko gasar ta ba su wata dama da babu kasar da ta samu irinta.
“Ga misali Ingila ita ce kasa daya tilo da har sai a wasan kusa da na karshe aka sa mata kwallo a zare.
“Na biyu ita ce kasa ta 13 da ta zama bakuwa a wasan karshe bayan Greece da Portugal kuma dukannin su sun dauki kofin a karon farko bayan sun kai wasan karshe.
“Na uku duk da cewa wasan ka iya zama 50-50 amma akwai wata dama da Ingila za ta samu a karon farko na magoya baya kamar yadda ta taba samu a shekara ta 1966.”
Sai dai Mubarak Abubakar cewa ya yi a nasa hasashen, Italiya ce za ta lashe gasar kamar yadda tun da farko ya yi hasashe.
“A tawa fahimtar, Italiya ce za ta cinye wannan gasa kamar yadda na yi hasashe tun kafin a fara gasar.
“Ingila suna da ’yan baya da gola masu kyau, hakan ya sa kwallo daya tal aka jefa a ragarsu; su ma Italiya golansu da ’yan bayansu ba kanwar lasa ba ne, domin kuwa sun fi na Ingila gogewa.
“Idan mun duba bangaren masu cin ball – idan ka cire Sterling da Kane a Ingila, kusan babu wani mai iya daukar alhakin cin ball, ba kamar Italiya da kusan kowa a tsakiyarsu ko saman su yana iya cin ball ba”.
Tarihi zai maimaita kansa
Sai dai Salisu Jegus ya kara kafa hujja da cewa, “Nasarar da Ingila ta samu da ci 2-0 a shekara ta 1977 wata alama ce da ke nuni da irin yadda kasar za ta maimaitta wancan sakamakon a filin wasa na Wembley wato tarihi zai maimaita kansa.”
Italiya za ta yi maganin Ingila
Game da yadda Italiya za ta danne Ingila, Mubarak cewa ya yi, “Da yawa daga kwallayen Ingila ta sama suke ci.
“Tsayin da ’yan bayan Italiya suke da shi, zai rage wa Ingila wannan dama. A daya bangaren kuwa, ’yan gaban Italiya ba sa bukatar sai sun yi yanka ko sun shiga yadi na 18 su ci ball, suna iya cin ball daga kowane wuri ko kusurwa.
“Idan muka yi duba ga tsakiyar fili, Italiya suna da gogaggun ’yan tsakiya masu wayo.
“Jorginho, misali, ya san Gasar Premier sosai. Don haka sarrafa tsakiyar filin ba za ta ba shi wahala ba.”
Mubarak ya karkare da cewa, “A karshe, ina hasashen Italiya za ta ci Ingila 1 – 0 ko 2 – 1!.”
Sai dai Salisu bai gamsu ba. “Daga karshe”, inji shi, “tun bayan kammala Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha kwallon kafa ta fara nunawa cewa kasar Ingila za ta iya jagorantar duniya a wasan nan ba da dadewa ba,” don haka a ganinshi Ingila ce za ta lallasa Italiya.
Ku fa, me kuke gani? Za ku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na musayar ra’ayi da muhawara, wato facebook.com/aminiyatrust, ko ku latsa hoton da ke kasa