Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe gasar Premier ta Ingila bayan shekaru 30 rabonta da ci gasar ba.
Hukumar gasar ta bayyana hakan ne bayan kungiyar Chelsea ta lallasa mai biye wa Liverpool din a matsayi na biyu, Manchester City da ci 2-1 a ranar Alhamis.
Liverpool ta lashe gasar ne ana saura wasanni bakwai a kammala buga gasar inda ta ba wa City din tazarar maki 23 a saman teburin gasar.
- Manchester City ta yi wa Liverpool kafar ungulu
- Liverpool tana zawarcin dan kwallon Najeriya Victor Osimhen
Tun kambun da ta lashe a shekarar 1990, Liverpool ba ta sake daukar gasar ba. A bara dai, kungiyar ta yi kokari sosai wurin neman cin gasar amma Manchester City ta samu nasara a kanta.
Liverpool ta ci wasanni 28 a cikin 31 da ta buga a gasar ta bana, wanda hakan ya sa dan wasanta na gaba Mohammed Salah ya bayyana cewa wannan ce damar kungiyar mafi girma ta lashe gasar.