A watan Janairun nan ne za a bude kasuwar saye da sayar da ’yan kwallon kafa a Nahiyar Turai. A lokacin ne wasu kungiyoyi za su fitar da makudan kudi don sayo ’yan wasan da za su taimaka musu lashe kofi ko wadanda za su hana su barin babbar gasa.
A wannan karo ko dan wasan wata kungiyar ya hadu da wata a gasar Zakarun Turai zai iya zuwa can ya buga mata kwallo. Ko hakan na nufin kungiyoyin sun daura damarar fitar da makudan kudi don kara karfin ’yan wasansu?
Kamar yadda shafin BBC Hausa ya wallafa, wani kamfanin zuba jari da kididdiga da ke Landan ya bayar da shawara ga kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya uku da ke kan gaba da fitattu 12 daga sassan Turai da duniya da ake ganin za su iya shiga kasuwa. A kididdigar kamfanin ya maida hankali kan kudin dan wasa da kokarin da ya yi wa wadda za ta sayar da shi da rawar da zai taka ga wadda za ta saye shi da kuma shekarun dan kwallo a tsakanin 26 zuwa 30.
Kamfanin ya bai wa BBC bayanai da sunayen wadansu ’yan kwallon da za su iya komawa wata kungiyar a watan Janairun nan.
PAUL POGBA: Mai shekara 26, na Manchester United, mai buga wasan tsakiya, kudin da yake a yanzu; Fam miliyan 85. Ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Real Madrid da Barcelona da kuma Jubentus.
CHRISTIAN ERIKSEN: Mai shekara 27 na Tottenham, mai buga wasan tsakiya. Darajarsa: Fam miliyan 51.4. Wanda ake alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Real Madrid da Manchester United.
OLIBIER GIROUD: Mai shekara 33, da yake bugawa a kungiyar Chelsea, kuma dan wasan gaba ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Inter Milan da Atletico Madrid.
LUCAS TORREIRA: Mai shekara 23, ya buga wa kungiyar Arsenal, dan wasan tsakiya ne. Darajarsa ta kai Fam miliyan 37.85, inda ake alakanta shi da kungiyar Napoli.
CENK TOSUN: Mai shekara 28, yana buga wa kungiyar Eberton, kuma mai buga gaba ne. Wanda ake alakanta zawarcinsa da kungiyoyin kwallon kafa na Leeds United da Crystal Palace da kuma Besiktas.
NATHAN AKE: Mai shekara 24, yana buga wasa a Bournemouth, mai tsaron baya ne. Darajarsa ta kai Fam miliyan 52. Ana alakanta shi da kungiyoyin Manchester City da Chelsea da kuma Tottenham.
WILFRIED ZAHA: Mai shekara 27, yana buga wa kungiyar Crystal Palace, dan wasan gefe daga gaba. A yanzu darajarsa ta kai Fam miliyan 41.1. kuma ana alakanta zawarcinsa da kungiyar Chelsea.
DWIGHT MCNEIL: Mai shekara 20, yana buga wa kungiyar Burnley, dan wasan tsakiya ne. Darajarsa ta kai Fam miliyan 24.75. kuma ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Tottenham da Newcastle da Crystal Palace.
DWIGHT GAYLE: Mai shekara 29, wanda ke buga wa Newcastle, dan wasan gaba ne. Ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin West Brom da Nottingham Forest da kuma Stoke.
RHIAN BREWSTER: Mai shekara 19, yana buga wa kungiyar Liberpool, mai wasan gaba ne. Ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Aston Billa da Crystal Palace da Leeds da kuma Swansea.
JADON SANCHO: Mai shekara 19, yana buga wa Borussia Dortmund, kuma mai buga gefe daga gaba. Darajarsa ta kai Fam miliyan 44.6.
Ana alakanta zawarcinsa da kungiyar Manchester City da Manchester United da Chelsea da Real Madrid da kuma Barcelona.
GARETH BALE: Mai shekara 30, yana buga wa kungiyar Real Madrid, dan wasan gaba daga gefe ne. Darajarsa yanzu ta kai Fam miliyan 44.7. Kuma ana alakanta zawarcinsa da kungiyoyin Tottenham da Manchester United.
TIMO WERNER: Mai shekara 23, yana guga wa kungiyar RB Leipzig. Darajarsa ta kai Fam miliyan 60.61. Kuma ana alakanta yiyuwar tafiyarsa zuwa Real Madrid ko Manchester United ko Chelsea ko kuma Liberpool.
EDINSON CABANI: Mai shekara 32, yana buga wa kungiyar Paris St-Germain, dan wasan gaba ne, wanda da ake alakanta shi da kungiyoyin Atletico Madrid da LA Galady.
THOMAS LEMAR: Dan shekara 24, wanda yake kungiyar Atletico Madrid, dan wasan gaba daga gefe ne, inda ake alakanta shi da tafiya zuwa kungiyar kwallon kafa ta Lyon.
NICOLO ZANIOLO: Mai shekara 20, yana wasa a kungiyar kwallon kafa ta Roma, dan wasan tsakiya ne. Darajarsa ta kai Fam miliyan 22, inda ake alakanta shi da tafiya kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ko Manchester United ko kuma PSG.
BEDAT MURIKI: Mai shekara 25, yana doka tamola a kungiyar Fenerbahce, dan wasan gaba ne da ake alakanta shi da tafiya kungiyar Leicester ko Tottenham ko Eintracht Frankfurt ko kuma Monaco.