✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasan Arsenal sun amince da zaftare albashi

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta zama ta farko a Gasar Premier da ta yi yarjejeniya da kocinta da ’yan wasanta a kan a zaftare…

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta zama ta farko a Gasar Premier da ta yi yarjejeniya da kocinta da ’yan wasanta a kan a zaftare musu albashi saboda coronavirus.

Ranar Litinin kocin kungiyar ta Arsenal, Mikel Arteta, da rukunin farko na ’yan wasan suka amince a zaftare kashi 12.5 cikin 100 na albashinsu.

Nasarar da kungiyar ta Arsenal ta yi ta samun Arteta da ’yan wasan su yarda a rage musu albashi dori ne a kan matsayar da Southampton da West Ham suka cimma da nasu ’yan wasan ta jinkirta biyan albashin.

“Muna farin cikin sanar da cewa mun cimma yarjejeniya ta radin kai da rukunin farko na ’yan wasa da kocinmu da sauran masu horar da ’yan wasa da nufin taimaka wa kungiyar a wannan lokaci mawuyaci”, Arsenal din ta bayyana a wata sanarwa.

Wannan yarjejeniya dai ta biyo bayan wasu jerin tattaunawa ne a makwanni biyu da suka wuce yayin da ’yan wasan Gasar Premier ke shan suka saboda kin da suka yi a rage musu albashi alhali wasu kungiyoyi sun fara sallamar ma’aikatan da ba sa buga kwallo don ririta kudin da suke da shi.

Hukumar gasar dai ta bukaci kungiyoyi su yi wa ’yan wasansu tayin zaftare kashi 30 cikin 100 na albashinsu, amma Kungiyar Kwararrun ’Yan Wasa ta ce hakan zai shafi harajin da ke shiga lalitar Hukumar Kula da Lafiya ta NHS.

An dai ce Arteta, wanda shi ma ya warke daga cutar coronavirus, shi ne ya shawo kan ’yan wasan na Arsenal.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa hukumomin Premier sun yi kiyasin cewa cutar coronavirus za ta jawo asarar fam biliyan daya (kwatankwacin naira biliyan 484).

A yanzu haka dai an dakatar da wasannin kwallon kafa a Ingila, kasancewar kasar na cikin dokar hana fita.