✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan uwana 5 aka kashe a harin kunar bakin wake a Borno

Mutane na cikin tashin hankali bisa halin da ’yan uwansu da harin kunar bakin waken ya ritsa da su

Al’ummar garin Gwoza da ke Jihar Borno, sun bayyana yadda ’yan uwansa da makusantansu suka rasu a harin kunar bakin wake da kungiyar Boko Haram ta kai wurin bikin daurin aure a garin.

Shehu Buba yana daga ’yan uwan wadanda harin kunar bakin wake ya rutsa da su da suka bayyana yadda suka rasa ’yan uwansu a harin da aka kai wurin liyafar daurin aure a ranar Asabar.

Ya shaida wa wakilinmu da ya ziyarci Asibitin Kwararru na Jihar Borno da ke Maiduguri inda a wadanda suka samu raunuka ke samun kulawa cewa, abin ya faru da sauri, “kamar mafarki ne.

“Na rasa mutane biyar a cikin iyalina cikin kasa da sa’o’i 24,” in ji shi.

Wakilinmu ya ga yadda jama’a ke cikin halin damuwa saboda halin da ’yan uwansu da aka kwantar suke ciki.

Buba Shehu, ya bayyana cewa, “Mutane uku ne suka mutu rabar Asabar sakamakon mummunan harin da dan kunar bakin wake ya kai a wajen liyafar daurin aure a gidanmu da ke Gwoza.

“Mun kuma samu kira a safiyar Lahadi cewa mutane biyu sun rasu sakamakon rashin jini a jikinsu.

“Don haka, ni kaina, na rasa ’yan uwa uku da abokaina biyu. Wannan yana da zafi,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Da yawa daga cikin abokanmu sun zo daga Maiduguri domin halartar daurin auren a Gwoza.

“Abin takaici, a halin yanzu bakwai suna karbar magani a wannan asibiti.

“A daren jiya daren Asabar, mutane 20 muka rasa, wasu 30  sun jikkata.

“An safiyar Lahadi, mun rasa kaein mutum daya a Maiduguri kuma ’yan uwanmu biyu sun mutu a Gwoza da sanyin safiya.”

Shi ma wani dan uwan wadanda abin ya shafa Abdul Umaru ya ce ya rasa mutane biyu yayin da wasu biyu da suka samu munanan raunuka, da a halin yanzu suke kwance ranga-ranga a asibiti.

“Na so halartar bikin aure amma ban samu abin hawa ba, kuma hakan ya sa na damu saboda rashin halartar bikin aure a gidanmu.

“Sai daga baya na ji an kai harin kunar bakin wake a wurin liyafar. Biyu daga cikin kawunnaina sun rasa rayukansu.

“A yanzu haka biyu ’yan uwana biyu na jinya a sakamakon raunukan da suka samu a hare-haren.

“Muna cikin tashin hankali da ganin ɗaruruwan mutane da ke nan wurin a cikin wannan halin.

“Abin bakin ciki ne, ka rabu da mutum babu jimawa sai ka ji an ce wasu marasa imani sun kashe shi.” in ji shi.

Aminiya ta gano cewa an kashe mutane da dama da suka hada da soja daya da kuma wasu bakin da suka halarci aure.

Wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon harin ’yan kunar bakin wake hudu a wurare daban-daban a garuruwan Gwoza da Pulka, duk a karamar hukumar Gwoza.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dokta Barkindo M. Saidu, jim kadan bayan faruwar lamarin, ya ce mutane 18 da suka hada da yara, manya, mata, da mata masu juna biyu sun mutu, yayin da wasu 19 da suka samu munanan raunuka aka kai su Maiduguri cikin motocin daukar marasa lafiya guda hudu.

Gwoza da ke kusa da dajin Sambisa da tsaunin Mandara, sun zama mafakar mayakan Boko Haram.

Yankin ya sha fama da munanan hare-hare a cikin kusan shekaru 15 da suka gabata.

Hare-haren kungiyar sun kashe daruruwan mutane, da dama sun jikkata, an kuma lalata gidaje, kasuwanni, asibitoci, ofisoshin ’yan sanda da sauran cibiyoyin gwamnati.

Amma an dade ba samu labarin harin kunar bakin wake ba, har zuwa ranar Asabar da ta gabata.

 

Daga Olatunji Omirin (Maiduguri), Haruna Gimba Yaya (Gombe), Sagir Kano Saleh, Saawua Terzungwe & Baba Martins (Abuja).