Wasu ’yan Ukraine sun dawo daga rakiyar sojojin kasar bayan da suka zargi sojojin da lalata kasar.
Bakhmut na daga cikin wuraren da aka ce sojojin sun lalata da hare-hare, lamarin da ya haifar da muhawara a tsakanin ’yan kasar, inda masu yabon sojojin da farko suka buge da ganin bakinsu.
- Zargin rashin lafiyar Atiku ya bar baya da kura
- Qatar 2023: Muhimman abubuwa kan karamar kasa mai tarin arziki
Wata ’yar kasar mai suna Yulia ta ce, ta yi amannar sojojin Ukraine sun jefa bama-bamai a wasu biranan nasu ne ganin Rasha na kokarin kwace yankunan.
“Na kasa gane wa lamarin nan, me ya sa Ukraine za ta rika lalata biranenta?”
“Na ji cewa Ukraine tana yin haka ne don tabbatar da Rasha ba ta samu komai daga gare ta ba,” in ji matar.
Bakhmut birni ne da ke yankin Donbas a Gabashin Ukraine, inda ’yan tawayen da ke samun goyon bayan Rasha suka fara rikici a shekara ta 2014, kuma ana yawan samun rarrabuwar kawuna a tsakanin mazauna yankin.
Rahotanni sun ce, saboda bacin rai kan abin da sojojin Ukraine suka aikata wa Bakhmut, ya sa wasu mazauna yankin suka koma nuna goyon bayansu ga sojojin Rasha.