✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘’Yan Taliban ba sa yarda su yi ido hudu da mata’

‘Ba sa yarda mu yi ido hudu, ko da kuwa da ni suke magana saboda ni mace ce.”

A lokacin da kungiyar Taliban ta jagoranci kasar Afghanistan tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001, Majalisar Dinkin Duniya ta yi uwa da makarbiya wajen fafutukar kwato hakkin mata a kasar.

A lokacin, daga cikin jami’an majalisar da suke kan gaba wajen fafutukar, har da wasu manyan jami’anta mata su biyu, daya daga cikinsu kuma ta yi aikin samar da agaji ne a kasar.

Radhika Coomaraswamy, wacce ta karade kasashe da dama, kuma ta yi aiki a Afghanistan a matsayin jami’a ta musamman mai yaki da cin zarafin mata tsakanin 1994 zuwa 2003, ta tuno yadda ta ce ’yan Taliban ba sa yarda su yi ido hudu da mata.

A wata tattaunawarta da kamfanin Dillancin Labarai na IPS Coomaraswamy ta ce, “Lokacin da na fara haduwa da Ministan Harkokin Wajen kasar, mun zauna gefe da gefe a kan wata doguwar kujera, kuma ya ki amincewa mu yi arba. Na yi ta kokarin mu hada ido, amma ya ki yarda.

“A lokacin ne daya daga cikin masu gadina ya zo ya rada min a kunne cewa Ministan ba zai yarda mu hada idanu ba.

“Lokacin da na hadu da Ministan Shari’a kuma, a kan rigingimun cikin gida, sai ya ce min ai matan Afghanistan suna da tarbiyya, ba sa iya kashe ko kuda, ballantana su yi fada da mazajensu,” inji Coomaraswamy, daya daga cikin manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya.

A wani labarin kuma, a lokacin da Anoja Wijeyesekera ta fara aiki a Afgahnistan a 1997 a matsayin jami’ar asusun UNICEF, takardarta ta fara aiki ta zo da wani kundi mai cike da ka’idoji, wanda ya bukaci ta rubuta ‘wasiyyarta’ kafin ta baro gida.

Anoja, wacce ita ce jami’ar UNICEF tsakanin 1997 zuwa 2001 a biranen Jalalabad da kuma Kabul, ta bayyana labarinta, makamancin na Coomaraswamy.

“Lokacin da na fara zuwa Afghanista a 1997 a matsayin jami’ar asusun UNICEF, jami’an gwamnatin Taliban sun ki amincewa mu yi ido hudu, saboda ni mace ce.

“Idan aka je wajen taro, wanda galibi dukkan mahalartansa maza ne, sai su kautar da fuskarsu daga waje na kwata-kwata, ko da suna magana da ni ne kuwa.

“Bayan wasu watanni da fuskantar irin wannan tarbar, wacce nake kallo a matsayin wasan kwaikwayo, sai muka fara hada idanu, kai har ma da musabaha, suka fara yi min Turancin Ingilishi sannan suka zama abokaina.

“Sai na rika cewa ma’aikatana watakila ’yan Taliban sun dauka na koma namiji ne,” inji ta, tana fada cikin raha.

A zamanin mulkin Taliban na baya dai, gwamnati ta hana mata yin aiki ko ma fitowa waje ba tare da wani namiji ya yi musu rakiya ba.

Sai dai a wannan karon, Taliban ta sha alwasjin cewa mulkin nata zai banbanta da na baya, musamman wajen ba mata ’yancin yin karatu da na yin aiki.

Babban abin jira a gani a yanzu dai shi ne ko Taliban za ta cika alkawuran ko kuma za a koma gidan jiya.