Wata wasika da ke yawo na cewa ’yan takarar da suka yanki tikitin neman zama Shugaban Jam’iyyar APC na kasa sun janye sun sallama wa tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu.
Takardar ta ce ’yan takarar su shida sun janye wa Abdullahi Adamu ne a jajibirin babban taron jam’iyyar, domin ya zama dan takara babu hammaya a zaben shugabannin jam’iyyar da za a gudanar a babban taron da ke gudanda a ranar Asabar.
- Kalubalen da ke gaban Jam’iyyar APC gabanin babban taronta
- Taron APC: Hadin kai ko dinkin gangar auzunawa?
A wasikar janyewar mai dauke da sanya hannun daya daga jin masu neman kujerar, tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, kuma Ministan Ayyuka na Musamma, Sanata George Akume, ya ce sun janye ne bisa bukatar Shugaba Buhari.
Wadanda suka janye din su ne tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko-Almakura; Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Sanata George Akume, Sanata Sani Musa Muhamma, Turaki Salifu Mustapha da kuma Etsu Muhammad.
Idan ba manta ba, Aminiya ta kawo rahoton cewa Abdullahi Adamu shi ne zabin Shugaba Buhari a cikin mutum bakwai da ke takarar shugabancin APC.
Akwai wasu mutum biyar kuma da yake so a ba wa kujeru a Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar.
A kan haka ne Buhari ya yi zama da gwamnonin jam’iyyar inda ya bukaci amincewarsu da ’yan gaban goshin nasa tare da bukatar su da su tattauna a tsakaninsu, su fitar da jerin mutanen da za a ba wa kujerun shugabanincin jam’iyyar ba tare da hamayya ba.
Kazalika ya yi zama da ’yan takarar shugabancin jam’iyyar, ya nemi su yi hakuri su mara wa Abdullahi Adamu, inda ya bukaci a mayar musu da kudadensu na takardar neman takara.
Buhari ya kuma yi makamanciyar zaman da ’yan Majalisar Dokoki da Kasa da kuma iyayen jam’iyyar domin ganin ba a samu baraka a taron dake gudana ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022 ba.