✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan takarar Gwamnan Gombe a kan sikeli

Ko a ’yan kwanakin nan Jam’iyyar NNPP ta karbi wasu fusatattun matan Jam’iyyar PDP.

Jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas a karon farko na mulkin farar hula a Jamhuriya ta Hudu ta zabi Gwamna na farko daga jam’iyyar da ba tare take da Gwamnatin Tarayya ba a 1999, wato Jam’iyyar APP, kuma jam’iyyar da ke mulki a matakin Tarayya ta kasance PDP.

Kuma wannan ne karon farko da jihar ta samu Gwamna farar hula, bayan da aka kirkire ta a matsayin jiha a 1996 da marigayi Shugaban Kasa, Janar Sani Abatcha ya yi.

Shigowar mulkin dimokuradiyya a 1999 aka zabi Alhaji Abubakar Habu Hashidu, ya zama Gwamnan farko na farar hula a Jam’iyyar APP na tsawon shekara hudu, sai kuma Gwamna Muhammad Danjuma Goje ya karba daga gare shi.

Gwamna Danjuma Goje ya mulki jihar na shekara takwas a Jam’iyyar PDP bayan ya gama ya zama Sanata.

Sai Gwamna Ibrahim Dankwambo ya gaje shi shi ma ya shekara takwas, kafin Kwamishinan Kudi da ya yi shekara bakwai a kan matsayin zamanin Gwamna Danjuma Goje wato Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya zama Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC kuma yanzu shi ne yake sake neman takara karo na biyu.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jam’iyyar APC

Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi shekara uku da rabi a karagar mulki kuma a yanzu yana kokarin sake dawowa a karo na biyu.

Kasancewarsa Gwamna kuma dan takara mutane da dama suna ganin yana da damar sake cin zabe.

Sai dai akwai masu ganin rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC ya sa ana zargin akwai masu yi masa zagon kasa don ganin ya fadi a zaben.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya

Masu hakan suna zargin abubuwa ba sa tafiya daidai inda suke takun saka da wasu jiga-jigan jam’iyyar, tun anazargin yi a boye har lamarin ya bayyana.

Masu nazarin siyasa suna ganin a wannan karo Jam’iyyar APC za ta fuskanci matsala a kokarinta na ganin ta lashe zaben mai zuwa saboda rikicin cikin gidan jam’iyyar da yadda al’amura ba sa tafiya daidai a bangaren ’yan siyasa a bangaren walwala da cin moriyar siyasa.

A cikin shekara uku Gwamna Inuwa Yahaya, ya yi wasu ayyuka masu dama musamman hanyoyi a kauyuka da gyara asibitoci, to amma a wurin’ yan siyasa ba aiki kawai ake bukata ba, har ma da walwala kuma suna ganin shi ne abin da aka rasa a Jihar Gombe.

A yanzu da zabe ke kara karatowa kuma ’yan siyasa ke sa tsammanin a ba su kudi don gudanar da wasu aikace-aikace don tallata dan takarar na APC, bayanai sun nuna har yanzu babu ko da kwamitin yakin neman zabe da aka kafa don fara hakan.

Alhaji Muhammad Jibrin Barde a Jam’iyyar PDP

A bangaren Jam’iyyar adawa ta PDP da Alhaji Muhammad Jibrin Barde, ke takara.

’Ya’yan jam’iyyar suna ganin zai iya cire musu kitse a wuta saboda yana yakin sunkuru da sauran ’yan takarar ba sa yi na bin mutane gida-gida yana ganawa da su da dare.

Alhaji Muhammad Jibrin Barde

Alhaji Dan Barde dan siyasa ne da ko a lokacin da yake takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a shekarar 2018 tare da Gwamna Inuwa Yahaya shi ne ya zo na biyu, a zaben fid-da-gwani kafin daga baya ya koma PDP, inda ’yan takara takwas ya lashe zaben fid-da-gwani don fafatawa da Gwamna Inuwa Yahaya na APC.

Duk da yadda ake ganin Alhaji Dan Barde, kamar bai shirya wa siyasar ba, shi kuma cewa ya yi gani kawai yake kamar ya zama Gwamna domin rashin fara yakin neman zabensa bai rasa nasaba da yadda yake ganinta ruwa-ruwa a kan Gwamna Inuwa Yahaya domin duk motsin da APC take yi kamar kamfe take yi wa PDP saboda rashin tabuka abin kirki.

Alhaji Khamisu Mailantarki na Jam’iyyar NNPP

A Jam’iyyar NNPP Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki ne, yake takarar Gwamna, kuma kafin zaman sa dan takara a jam’iyyar ya nemi kujerar a APC, kafin ya fita daga jam’iyyar ya koma sabuwar Jam’iyyar NNPP.

Alhaji Khamisu Mailantarki, ya taba zama dan Majalisar Wakilai a shekarar 2011 da kuri’u masu yawa da aka ce duk Najeriya babu wanda ya samu kuri’u kamarsa a CPC, kuma ba tare da yana da ubangida a siyasa ba, yanzu ma haka yake ganin kamar tarihi zai iya maimaita kansa.

Alhaji Khamisu Mailantarki

Yanzu haka ya fara yawon yakin neman zabe a kasuwanni da tashohin mota kuma duk da cewa jam’iyyarsa sabuwar jam’iyya ce, amma ta fara karbar wadanda suka canja sheka daga Jam’iyyar PDP.

Ko a ’yan kwanakin nan Jam’iyyar NNPP ta karbi wasu fusatattun matan Jam’iyyar PDP da suka kasance tsofaffin shugabanin matan jam’iyyar a baya.

Sannan akwai masu cewa yadda Mailantarki ke kara karbuwa a wajen jama’a tamkar yana sharar fage ne na in ma bai ci zaben Gwamna a shekarar 2023 ba, a zaben shekarar 2027 zai iya lashe zaben Gwamnan jihar a duk jam’iyar da ya fito.