Wani hari da ake zargin ’yan ta’addan ISWAP da kai wa da makamin roka a garin Damboa na Jihar Borno, ya yi sanadiyyar kashe mutum 5, wasu 11 kuma sun jikkata.
Wasu kwamandojin ’yan ta’addan biyu suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) hakan ranar Lahadi.
- Bayan shafe shekara 320, an daina buga jarida mafi dadewa a duniya a kan takarda
- Ba da yawunmu aka kona Alkur’ani ba, muna Allah wadai – Gwamnatin Sweden
Mayakan da dama sun yi yunkurin kutsawa garin Damboa da yammacin ranar Juma’a, amma suka fuskanci tirjiya daga sojojin Najeriya da na farar hula na CJTF.
Harin dai shi ne na baya-bayan nan a rikicin Boko Haram da ISWAP na Najeriya na tsawon shekaru 14 a yankin Arewa maso Gabas, inda mutane 40,000 suka mutu yayin da sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu.
Babakura Kolo, wani Shugaban ’yan banga a yankin ya ce: “Saboda bacin rai, ’yan ta’addan sun harba gurneti a garin daga nesa, wanda ya kashe mutane biyar tare da raunata wasu 11.”
“An binne mutanen biyar da suka mutu a ranar Asabar, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa babban birnin Jihar na Maiduguri a cikin wani jirgi mai saukar ungulu domin kula da lafiyarsu,” in ji Ibrahim Liman, kwamandan mayakan na biyu.
Sai dai sojojin Najeriya, wadanda dakarunsu ke garin suna gadin sansanin sojin, ba su amsa kiran neman karin bayani da aka musu ba.
Garin Damboa dai na da tazarar kilomita 90 kudu da Maiduguri, wanda ke gefen dajin Sambisa, wani kungurmin dajin da ke dauke da dimbun namun daji da ya zama sansani ga ’yan ta’addan, kuma ya sha fama da hare-haren ’yan ta’addan.
Duk da cewa kungiyar ta Boko Haram da kishiyarta ta ISWAP, suna kai hare-hare da bama-bamai a kan wuraren da sojoji ke kai hari, amma ba kasafai suke amfani da su kan fararen hula ba sai lokaci zuwa lokaci.
A lokuta da dama kungiyar Boko Haram ta yi ta harba rokoki kan Maiduguri a yunkurinta na karbe birnin. Na baya-bayan nan shi ne a watan Fabrairun 2021, inda aka kashe mutum 10 sannan kusan 60 suka jikkata, a cewar wani jami’in tsaron da ya nemi a sakaya sunansa.