✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba da yawunmu aka kona Alkur’ani ba, muna Allah wadai – Gwamnatin Sweden

Gwamnatin ta ce tana mutunta 'yancin yin addini

Gwamnatin Sweden ta yi Allah wadai da yadda aka kone Alkur’ani a birnin Stockholm na kasarta, inda ta ce ba da yawunta aka yi hakan ba.

A ranar Babbar Sallar bana (Laraba) ce dai aka kone littafin, wanda shi ne mafi tsarki ga Musulmai, a kofar babban masallacin birnin na Stockholm.

Martanin kasar na zuwa ne kwana daya bayan Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi Allah wadai da lamarin, sannan ta yi kira da a dauki tsattsauran matakin kiyaye sake aukuwar hakan a nan gaba.

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar ranar Lahadi, gwamnatin ta ce, “Gwamnatin kasar Sweden ta lura da yadda aka nuna kin jinin Musulunci a yayin zanga-zangar da aka yi.

“Muna Allah wadai da wannan lamari da kakkausar murya, kuma wannan ya saba da ra’ayin gwamnatin Sweden.

“Kone Alkur’ani ko kuma kowanne littafi mai tsarki laifi ne, rashin da’a ne kuma yunkuri ne na tunzurawa da fusata mutane. Nuna wariyar launin fata, kin jinin wata kabila ko addini ba shi da muhalli a Sweden ko ma kowacce kasar Turai,” in ji sanarwar.

Kasar ta kuma ce kundin dokokinta sun bayar da ’yancin yin addini ko shigwa kowacce irin halastacciyar kungiya ba tare da kyama ba, kuma za ta ci gaba da kokarin tabbatar da hakan a zahiri.

Sanarwar dai na zuwa ne bayan OIC, kungiyar Musulmai mai mambobin kasashe 57, ta yi kira da a dauki mataki na bai-daya kan aikata hakan a nan gaba.

Tuni dai kasashe irin su Iraki da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Maroko suka yi wa Jakadunsu da ke Sweden kiranye a wani mataki na nuna rashin amincewarsu da lamarin.