Mambobin wata kungiya mai matukar nuna kiyayya ga Musulunci a Denmark sun kona Al-Qur’ani da tutar kasar Iraki a yayin da duniya take ci gaba da Allah wadai bisa kona littafin mai tsarki a Sweden.
’Yan kungiyar mai suna Danske Patrioter sun kona Al-Qur’anin ne a wajen Ofishin Jakadancin Iraki da ke Copenhagen, babban birnin kasar ranar Juma’a.
- Iraki ta kori Jakadan Sweden saboda kona Al-Qur’ani
- An harbe mutum 2 wajen warwason kayan abinci a Taraba
Kazalika sun rike kwalaye da aka yi rubutu da ke zagin Musulunci da Musulmai, sannan suka fito da Al-Qur’ani mai tsari da tutar kasar Iraki suka kona su bisa kariyar ’yan sanda, kamar yadda bidiyoyin da aka watsa a soshiyal midiya suka nuna.
’Yan kungiyar sun ce sun dauki matakin ne domin mayar da martani ga harin da aka kai a Ofishin Jakadancin Sweden da ke birnin Bagadaza.
Ranar Alhamis da sassafe, dandazon masu zanga-zanga a Iraki sun cinna wuta a Ofishin Jakadancin Sweden da ke Bagadaza don nuna fushinsu ga kona Al-Qur’ani da wani mutum mai suna Salwan Momika ya yi a Sweden ranar 28 ga watan Yuni daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar Layya.
Mutumin Kirista ne dan asalin Iraki wanda aka haifa a Sweden.
A gefe guda, Turkiyya ta bayar da umarnin a kamo mata dan siyasar nan na kasar Denmark Rasmus Paludan da mutum tara wadanda ake zargi da kona Alkur’ani a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Stockholm a watan Janairu, a cewar ministan Shari’ar Turkiyya.
“Ofishin Babban Mai Shigar da Kara ya bukaci a yi bincike mai zurfi domin gano wadanda ake zargi da kuma samo shaidun da suka nuna cewa an aikata wannan laifi,” in ji Ministan Shari’a Yilmaz Tunc.
An yi zanga-zanga a Iraki
Daruruwan mutane sun yi yunkurin shiga yankin Green Zone a Bagadaza, wani yanki mai dimbin ofisoshin jakadancin kasashen waje da kuma wurin zama na gwamnatin Iraki.
Kusan masu zanga-zanga 1000 ne jami’an tsaro suka tarwatsa a safiyar ranar Asabar, sakamakon rahotannin kona Al-Qur’anin da aka yi a gaban Ofishin Jakadancin Iraki da ke Denmark.