✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Shettima ya isa ƙasar Sweden

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa ƙasar Sweden, inda zai tattauna da gwamantin ƙasar kan harkokin kasuwanci da Nijeriya

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya sauka a ƙasar Sweden, inda ya kai ziyarar aiki na kwana biyu domin ƙara ƙulla a tsakanin ƙasashen.

A yayin ziyarar, Shettima zai tattauna da Firaminista da manyan jami’an gwamnatin Sweden domin ƙara ƙulla dangantakar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Zai kuma gana da Gimbiya mai jiran gado, Victoria a yayin ziyarar, wadda ya samu rakiyar Gwamnan Filato Caleb Mutfwang da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnatin Nijeriya.