Akalla mayakan kungiyar ISWAP 82 sun nitse a wani kogin da ke garin Damasak na Jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan da iyalansu daga yankin Tafkin Chadi sun nitse ne a kokarinsu na guje wa babban mamayar da sojoji suka yi wajen farauto su a tsakanin ranakun 2 zuwa 3 ga watan Yunin 2023.
- Ma’aikatan shari’a za su tsunduma yajin aiki kan janye tallafin mai
- Daula Hotel: Kamfanin da ke gini na neman diyyar N10bn daga Gwamnatin Kano
Suna kokarin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar ne don tsira da rayuwarsu lokacin da suka hadu da ajalin nasu.
Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa an samu faruwar lamarin tsakanin al’ummomin Bulama Modori, Kaneram, Dogomolu da Jokka.
Wannan kogi da ’yan ta’addar suka nutse a ciki ya ratsa ta kogin Komadougo Yobe, zuwa Tafkin Chadi, sannan ya shiga Jamhuriyar Nijar.
Majiyar ta ce ’yan ta’addan sun yi yunkurin tserewa ne saboda fargabar kada hare-haren da dakarun Najeriya da na rundunar MNJTF ya rutsa da su a sakamakon labarin da suka samu dangane da farmakin da sojojin suka kaddamar a yankin da nufin share su daga doron kasa.
Yawancin wadanda suka mutu dai mata ne da kananan yara wadanda ba su iya yin iyo ba, yayin da wasu da dama ke samun sauki sakamakon wahalar da suka sha cikin kogin kafin su tsira.
Ya zuwa yanzu dai, majiyar ta ce ana ci gaba da gano wasu gawarwakin na mata da na kananan yara da kuma wasu daga cikin ’yan ta’addan na ISWAP da ba su iya fitar da kansu ba.