’Yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno sun kashe wasu manoma da ke aikin gona tare da arcewa da wasu karin mutane uku a yankin Gwoza.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Timta yayin tattaunawarsa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin Jihar.
- Babu cin naman kare a Musulunci – Sheikh Gumi
- Cikin kwana 45, kuɗin Abdussamad Rabi’u sun ƙaru da Naira biliyan 820
Sarkin ya ce, ’yan ta’adda sun kashe mutum biyar a gonakinsu da ke tsakanin garin Gwoza da yankin Limankara na yankunan Patwe da tsaunin Tangerang a karshen makon da ya gabata.
Ya ce abin takaici ne yadda aka sake samun sabon salo na kai farmaki daga maharan inda ya ce har ma sun yi awon gaba da wasu mutane uku a kan hanyarsu ta zuwa maboyarsu.
Sai dai ya mayar da martani ga wasu wallafe-wallafen da aka buga a wata kafar sadarwa ta zamani cewa daruruwan mazauna garin sun mamaye fadarsa tare da nuna rashin amincewarsu kan sabbin kashe-kashen da ’yan ta’adda ke yi wa manoma.
Uban kasar wanda ya kuma ce daga bisani ’yan ta’addan sun kashe daya daga cikin wadanda suka sace, yayin da sauran mutanen biyun ba su san inda suke ba a yankin dutsen.
Timta ya yi nuni da cewa lamarin abin takaici ne kuma abin Allah wadai ne, musamman a yanzu da damina ta zo kuma akasarin mutane sun shiga aikin noma domin rayuwa.
Lamarin dai ya jawo hankulan jama’a inda suka kai ziyarar ta’aziyya ga sarkin a fadar da ke garin Gwoza mai tazarar kilomita 130 daga Maiduguri.
A cewarsa, gaba dayan Karamar Hukumar Gwoza da babban birninta na karkashin ikon Boko Haram ne, har zuwa lokacin da sojoji suka kwato ta a watan Maris, 2015 har zuwa yau da mazauna yankin ke iya gudanar da rayuwarsu cikin walwala da sauki.