✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja

Ana zargin ’yan ta’adda sun yi wa wani mafarauci mai shekaru 47, Wabari Ukpaka yankan rago a yankin Chiji da ke Karamar Hukumar Abaji a…

Ana zargin ’yan ta’adda sun yi wa wani mafarauci mai shekaru 47, Wabari Ukpaka yankan rago a yankin Chiji da ke Karamar Hukumar Abaji a birnin Abuja.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis ta makon shekaran jiya yayin da mamacin ya fita farautar naman dawa da misalin karfe 4.00 na Yamma a wani daji da ke yankin.

Ya ce mamacin ya ajiye baburinsa a wata gonarsa gabanin ya shiga farautar naman dawa a dajin dauke da wata bindigarsa kirar gida amma wasu ’yan ta’adda suka bi shi har ciki suka yi masa yankan rago.

“A gaskiya ’yan uwansa sun yi ta zuba idanu wajen ganin dawowarsa a gida a wannan rana a yayin da ya fita farautar naman da za a yi amfani da shi na bikin Kirsimeti, sai gawarsa aka tsinto da Yammacin ranar Juma’a a cikin daji an yi masa yankan rago,” inji shi.

Wani dan uwan mamacin ya shaida wa Aminiya cewa babu alamar rauni na harbin bindiga da aka samu a jikinsa, sai dai ya tabbatar da cewa an yi amfani da wani abu mai kaifi wajen yanka makogwaron mamacin.

“A hakikanin gaskiya, babu wata alamar rauni na harbin bindiga a jikinsa lokacin da muka fita nemansa, sai dai mun riske shi ne da yanka a makoshinsa sannan aka jefar da gawarsa a wurin da mutane za su gani cikin sauki,” inji shi.

Yayin da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ta ce suna ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.