Gwamna Katsina, Aminu Bello Masari ya koka cewa ’yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi 10 a jiharsa, inda suke wa mata fyade a kullum.
Masari ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, inda ya bukaci sojoji su da sauran hukumomin tsaro su matsa kaimi wajen tsare rayuwar al’ummomin yankunan.
- Abin Da Ke Saka ’Yan Najeriya Shakku Game Da COVID-19
- Labarin rataye kai ya sa malamai nadama a Zariya
Ya ce yana cikin tsananin damuwa saboda halin da ake cikin na tsaro a yankunan, inda ya ce sujoji da sauran jami’an tsaro na bukatar kayan aiki don magance matsalar ta’addanci a jihar.
Gwamnan ya kara kira ga sauran hukumomin tsaro da su kara zage damtse a kan kokarin da suke yi na baya don a mai da sojoji bariki ta yadda ’yan sanda za su ci gaba da kula da tabbatar da bin doka da oda.
– Muna cikin tsananin damuwa
A cewara, “A nan Katsina idan muka ce muna jin dadi mun yaudari kanmu, a cikin mayuwacin hali muke saboda yawan garkuwa da mutane, satar shanu, yi wa mata fyade da kuma fashi a kan manyan titunanmu.
SAURAI: Abin da ke sa ’yan Najeriya shakku game da COVID-19:
“Muna bukatar a yi amfani da sabuwar fasahar zamani sosai wajen ganin an dakile ayyukan ta’addanci a jihar nan.
“Ba za mu ci gaba da yaudarar kanmu cewa za mu iya korar ayyukan ta’addanci a jihar nan ba.
“A baya ba a taba cin wannan nasarar ba, saboda haka yanzu ma ba za mu iya ba, amma mun san da karfinku za mu iya a nan gaba.
“Mun san ko ba ku magance shi duka ba za ku rage ta matuka ta yadda za ta daina addabar mutanen jihar.
“10 daga cikin Kananan Hukumomi 34 na Jihar Katsina suna fama da ’yan ta’adda wadanda suke kai farmaki kullum, wanda hakan ke hana mu barci.
“Shi ya sa ba ma iya kashe wayoyinmu saboda mus an me ke faruwa a kananan hukumomin; da mun tashi da safe kafin in yi komai sai na san me ke faruwa na kananan hukumomin.
– Sojoji sun gode wa Katsinawa
A nasa bangaren, Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya yi jinjina kan yadda sojoji suke samun kayan aiki, hadin kai da mu’amala mai kyau daga gwamnati da kuma mutanen Katsina.
Ya kara da cewa ya zo jihar ce don gane wa idonsa yadda abubuwa suke tafiya a yankin Arewa Maso Yamma.
“Na kawo wannan ziyarar aiki ne zuwa Runduna ta 8 a Jihar nan domin in fahimci halin da ake cikin bayan na kama aiki a watan Mayu sakamakon rasuwar tsohon Babban Hafsammu, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru.”
Ya kara da cewa duk lokacin da sabon shugaba ya ziyarci dakarunsa a bakin daga don ya gane wa idonsa, zai tattauna da su don ya san matsalolinsu ya kuma kara sumu karin gwiwa.
“Na zo nan ne don jinjinawa da kuma gode muku saboda abin da kuke wa sojojinmu na ba su kayan aiki da kuma kara ba su shawarwari idan hakan ya kama.
“Ina matukar godiyata ga gwamna, kar ka gaji da kokarin da kake wajen taimaka mana.
“Kuma ni ma zan kara neman hadin kan takwarorinmu na sauran hukumomin tsaro, ta hakane za mu shawo kan matsalar tsaron da take addabarmu,” inji shi.