✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan ta’adda sun kashe sojojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa a Abuja

Hafsan soja da wasu kananan sojojin daga rundunar da ke tsaron shugaban kasa sun rasu, wasu sun sha da kyar a hannun ’yan bindiga a…

Wani hafsan soja mai mukamin Kyaftin tare da kananan sojoji biyu daga Rundunar da ke Tsaron Shugaban Kasa sun kwanta dama a harin ’yan bindiga a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sojojin daga Rundunar da ake kira ‘7 Brigade of Guard Nigerian Army’ sun gamu da ajalinsu ne a harin kwanton bauna da ’yan bindigar suka yi musu a Abuja.

Hakan na zuwa ne kimanin awa 24 bayan ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Majiyarmu ta soji ta shaida mana a ranar Litinin cewa lamarin ya rutsa da sojojin ne bayan sun samu kiran dauki daga Makaran Koyan Aikin Lauya da ke Bwari a Abuja.

A ranar Lahadi ce suka samu kiran bayan hukumar makarantar ta samu wasikar barazanar hari daga ’yan bindiga.

Majiyar ta ce, “Bayan samun wasikar barazanar ce hukumar makarantar ta sanar da hukumomin sojin Rundunar 7 Guards Brigade.

“An tura Kyaftin din tare da wasu sojoji zuwa makarantar domin gudanar binciken sharar fage, inda suka gana da hukumar makarantar kan matakan da za a dauka domin tabbatar da tsaron dalibai da malamai da kayan aiki.

“Abin takaci a hanyarsu ta komawa ce aka yi musu kwanton bauna aka kashe Kyaftin din da kananan sojoji biyu”.

Ta kara da cewa sauran sojojin da ke cikin ayarin kuma sun sha da kyar a harin ’yan ta’addar.

Abin kunya

Bincikenmu ya gano masu ruwa da tsaki sun bukaci kar a bayyana abin da ya faru da sojojin da kuma barazanar da makarantar take fuskanta.

“Sun bukaci hatta ma’aikatan makarantar kar a bari su sani domin zai zama abin kunya ga gwamnati,” kamar yadda majiyar ta bayyana.

Majiyar ta ce a sakamakon barazanar, hukumomi na kokarin girke jami’an tsaron hadin gwiwa domin kare makarantar d ana daukacin yankin Bwari.

Ta bayyana cewa abin da ya faru ya sanya mazauna yankin cikin fargaba, musamman masu zama a cikin makarantar ta koyon aikin lauya da kuma gine-ginen gwamnati.

Abuja na cikin barazana

“Wannan ita ce kololuwar hari da aka kai a Birnin Tarayya, Abuja,” a cewar majiyar sojin.

“Amma tun ba yanzu ba akwai wannan barazana, domin babu wani mutum a fannin tsaro da zai ce bai san da barazanar da gaba daya Abuja ke ciki ba.

“’Yan ta’adda sun kafa sansanoni a wurare daban-daban a Abuja, shi ya sa ake samun garkuwa da mutane a wurare iri Kuje, Gwagalada da sauransu a cikin shekara guda.

“manufarsu ita ce kunyata gwamnati.
Suna sheke ayarsu a wasu wuraren a Abuja, ga shi yanzu lamarin ya zo nan,” a cewarsa.

Sojoji sun tabbatar da harin

Sojoji sun tabbatar da harin da ya yi sanadiyar mutuwar Kyaftin din da kananan sojoji a hanyar Bwari.

Kakakin Rundunar Guards Brigade, Kyaftin Godfrey AnebiA bakpa, ya tabbatar da harin da cewa sun tura dakaru domin gudanar da sharar yankin da abin ya faru domin kakkabe duk wasu ’yan ta’adda.

Hare-haren ’yan bindiga a Abuja

A baya-bayan nan ana yawan samun hare-haren ’yan ta’adda kauyukan babban birnin Tarayya.

Daga ciki sun yi garkuwa da wani basarake a yanki Kucihbuyi, a Karamar Hukumar Bwari.

A kwanakin baya, ’yan ta’adda sun kai hare tare da sakin daruruwan fursunoni a Gidan Yarin Kuke.

Akwai kuma hare-haren da suka tilasta wa mazauna yin kaura a kauyukan Abaji, Kuje da Kwali.

Ko a ranar Litinin sai da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta rufe Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali bayan harin ’yan bindiga a kusa da makarantar.