’Yan bindiga sun kashe sojoji hudu da suke rakiyar wasu ma’aikatan kamfanin mai a Jihar Ribas.
Mukkaddashin Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta 6, Manjo Danjuma Jonah, ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a yankin Enweh West da ke Karamar Hukumar Ahoada ta Gabas ta Jihar.
Ya ce a yayin musayar wuta a ranar Talata ne sojoji hudu suka kwanta dama, biyu daga cikin ma’aikatan kamfanin man kuma ba a gan su ba.
Manjo Jonah ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a kan hanyar Amungboro zuwa Emuphan, inda “maharan suka tsere ta Kogin Orashi.
- Hayaniya ta kaure a Majalisar Kano kan kudaden masarautu
- Kano: An kama Daraktan ma’aikatar ruwa kan karkatar da injinan rarraba ruwa
“Sojoji na ci gaba da yin sharar wurin domin kamo maharan da kuma gano ma’aikatan kamfanin man da ba a gani ba.
“Baban Kwamnadan Runduna ta 6 Manjo-Janar Jamal Abdussalam, ya jinjina wa sojojin da suka rasu, tare da yin Allah-wadai da harin,” in ji Danjuma Jonah a sanarwar da ya fitar a daren Talata.