✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe mutum bakwai a garin Gboko

Hukumar ’yan sanda a Jihar Biniwai ta bayyana cewa mutum bakwai aka kashe a garin Gboko, a ranar Larabar da ta gabata a yayin da…

Hukumar ’yan sanda a Jihar Biniwai ta bayyana cewa mutum bakwai aka kashe a garin Gboko, a ranar Larabar da ta gabata a yayin da wasu da ake tsammanin ’yan ta’adda ne suka far wa mutane a tashar mota. A sakamakon haka, Gwamnan Jihar, Samuel Ortom ya sanya dokar hana yawon dare a garin na Gboko da al’amarin ya faru.

A jawabinsa ga manema labarai, Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Fatai Owoseni ya bayyana cewa wannan al’amari bai da alaka da addini ko kabilanci, aiki ne na ’yan ta’adda. Ya bayyana cewa, “Da misalin karfe 11 na safiyar Laraba, mun samu rahoton cewa babu lafiya a garin Gboko, inda wani al’amari ya faru daidai misalin karfe 9 zuwa 10 na safiyar ranar, cewa wasu ’yan ta’adda sun far wa wasu Fulani, suka kashe su a tashar mota, a lokacin da suke kokarin shiga mota zuwa wani gari.

“An far wa mutanen ne a tashar mota, a yayin da suke shirin shiga mota zuwa Okene, wasu kuma suka ce Taraba za su. ’Yan sanda sun halarci wurin a lokacin da suka samu labarin faruwar al’amarin, inda kuma su ’yan ta’addar suka rika jifar ’yan sanda da duwatsu.

“Mun je wurin ne da nufin tantance abin da ya faru. Mun samu bayanin da zai taimaka mana mu kamo wadannan ’yan ta’adda kuma muna kallon wannan aika-aika a matsayin ta’addanci amma ba ya da nasaba da addini ko kabilanci,” inji Kwamishina.

 daya daga cikin mazauna garin Gboko, wanda kuma ya gane wa idonsa gawarwakin mutanen bakwai da aka kashe, ya bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya faru. “Game da wannan al’amari kuwa, wasu mutane ne suka shiga tashar motar Gboko da nufin samun motar da za su shiga zuwa wani gari. Sun gaya wa abokina da ke bakin tashar cewa sun fito daga Jalingo ne za su wuce Akure.”

Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron kada a kai masa farmaki ya kara da cewa “Mutanen sun ba su kashi sosai, inda nan take uku cikinsu suka mutu, inda sauran hudu suka mutu daga baya. Yanzun nan muke dawowa daga jana’izarsu. Tun da barko, an kai gawarwakin nasu ajiya a asibiti amma mutanen da suka kashe su suka je da karfin tsiya suka fito da su, suka kone su.”