Wani rahoto na musamman ya nuna ’yan ta’adda sun kashe akalla mutum 55,430 a sassan Najeriya daga hawan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 zuwa yanzu.
Hakan da ke kunshe cikin rahoton da kafar Daily Trust ta ruwaito, na nufin a kowace rana ’yan ta’adda na kashe kimanin mutun 20 — a kwana 2,743 da gwamnati mai ci ta yi a kan mulki zuwa yanzu — a sassan kasar da ke fama da matsalolin tsaro.
- Rikicin siyasa ya ci rayuka 1,525 a Najeriya —Rahoto
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023
Rahoton ya nuna daga hawan gwamnatin a 2015 zuwa yanzu, ’yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka sun ajalin mutum 55,430 a sassa daban-daban na Najeriya.
Matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da su sun da ta’addancin Boko Haram wanda ya faro tun daga shekarar 2009, da hare-haren ’yan bindiga da rikicin bakilanci, da na addini da na manoma da makiyaya, da ta’addancin kungiyar IPOB mai neman ballewa daga kasar da kuma rikice-rikicen siyasa.
A wani rahoto da cibiyar Tony Blair ta fitar ta bayyana cewa daga 1999 da aka dawo kan tafarkin dimokuradiyya a Najeriya zuwa yanzu, an kashe akalla mutum 1,525 a sakamakon rikice-rikicen siyasa a kasar.
Cibiyar Tony Blair ta bayyana cewa alkaluman kashe-kashe da aka samu daga zaben 1999 zuwa yanzu abin damuwa ne lura da karatowar babban zaben 2023 a Najeriya.
Rahoton na zuwa ne mako biyu bayan Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce a cikin kwana 50 an samu tashe-tashen hankula 52, yana mai gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, hakan zai iya kawo tasgaro ga zaben 2023.
Kungiyar Sanya Ido kan Zabuka ta Tarayyar Turai (EU), ta ce, “rikici da barazanar magoya bayan jam’iyyu ga masu zabe da jami’an hukumar zabe ta INEC” sun dabaibaye zaben 2019.
Ko da yake, a hukumance babu tabbatattun alkaluman tarzomar siyasa da rikice-rikicen kabilanci daga 2015 zuwa 2019 a Najeriya.
Rahoton da kafar Daily Trust ta samu ya nuna rikicin zaben 2011 ne mafi muni, inda tarzoma da aka yi na kwana uku, ya yi ajajlin mutum 800, wasu 65,000 kuma suka rasa muhallansu.
Na biye da shi shi ne zaben 2003, inda mutum 300 suka rasa rayukansu, na uku shi ne zaben 2019 da aka kashe mutum 145, sannan aka yi asarar rayuka 100 a zaben 2015.
A 2003 an rasa mutum 100 bayan a zaben 1999 mutum 80 sun rasa rayukansu sakamakon rikice-rikice siyasa.