Wasu sojoji Uku sun tsallake rijiya da baya a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a Jihar Edo.
Gwamnatin jihar ta sanar cewa ’yan bindiga sun kai wa sojojin hari ne a wani kamfanin manja da sojojin suke fadi a Karamar Hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Chris Nehikhare, ya ce daya daga cikin sojojin yana halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, sauran biyu kuma samu munanan raunuka.
Ya sanar a lokacin da ya je dubiyar sojojin a asibiti ya ce an kai musu hari ne a kamfanin manja na Okomu Oil a ranar Juma’a.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Tamowa Ke Nema Ta Gagari Kundila A Arewa
- Ta yi iƙirarin rashin ci da sha a sama da shekara 16
A cewarsa, hukumomin jihar na yin abin da ya kamata domin kawar da duk ’yan ta’adda da ke shiga rigar kungiyoyin asiri da dangoginsu.
Nehikhare ya kara da cewa an kafa rundunar aiki da cikawa ta musamman domin wannan aiki karkashin jagorancin Daraktan hukumar naD DSS.
A cewar kwamishinan, Gwamna Godwin Obaseki ya yi alkawarin biyan kudi jinyar sojojin da kuma daukar matakan da za su zama darasi kan duk masu kunnen kashi da ke kai irin wadannan hare-hare a jihar.