Masu garkuwa da mutane sun dauki wani sabon salo inda a yanzu ’yan ta’addan suke yaudarar kananan yara su shigo cikinsu a Jihar Sakkwato.
A kwanakin baya ne wasu masu garkuwa da mutane suka yaudari wasu kananan yara biyu daga kauyen Baliyo da ke Karamar Hukumar Binji ta jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, kananan yaran na daga cikin mutane 15 da rundunar ’yan sandan jihar ta gabatar kan zargin yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.
Ana kuma zargin wasu mutum biyu, wadanda su ne iyayen gidan kananan yaran, da laifin yin garkuwa da wasu mutane uku.
- An kashe kasurgumin dan bindiga Mai Dubu-Dubu a Sakkwato
- Hanyoyin Kauce Wa Manyan Cututtuka A Lokacin Zafi
- An Sako Murja Kunya daga gidan yari a Kano
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Hayatu Kaigama, ya bayyana cewa bayan ’yan bindigar sun sace mutanen sun kai su wani wuri a cikin daji, sai suka gayyaci yaran biyu don yi musu gadin su.
Daya daga cikin kananan yaran ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ’yan sandan Jihar Sakkwato cewa “Muna kiwon dabbobi sai Jemmu da Usman suka zo a kan babur suka dauke mu zuwa cikin daji inda aka ajiye wasu mutane uku da aka sace, suka bukaci mu lura musu da mutanen.
“Bayan mun yi gadin mutanen na wani lokaci sai masu garkuwar suka dawo daga cikin gari, sai muka baro wurin, kuma tun daga lokacin ba mu sake komawa wurin ba,” in ji shi.
Ana zargin wadanda aka sacen an shigar da su dajin ne aka daure su da igiya kafin a gayyato yaran su tsare su.
Daya daga cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen, ya shaida wa manema labarai cewa kananan “Yaran sun ambaci sunana ne kawai a matsayin mai garkuwa da mutane, amma ban taba sace kowa ba a rayuwata.
“Abokina da aka kama mu tare zai iya shaida cewa ni ba mai garkuwa da mutane ba ne; Allah Shaida ne cewa ni ba mai garkuwa da mutane ba ne,” inji shi.
Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya tabbatar da cewa sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan 10 a kan kowanne daga cikin mutane ukun da aka sace kafin aka sako su.
Kaigama ya bayyana cewa uku daga cikin wadanda ake zargin sun amsa laifin, yayin da na hudu ya nesanta kansa da laifin.
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar ’yan sanda sun kammala bincike.