✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun aika mutane 26 lahira a Kastina

’Yan sanda sun tabbatar cewa an kashe mutane 11 a kauyen Unguwar Lamido da ke yankin Karamar Hukumar Bakori

Akalla mutane 26 ne ’yan ta’adda suka kashe a wasu kauyuka biyu da ke kananan hukumomin Bakori da Kankara a Jihar Katsina.

Shaidu a karamar hukumar Kankara sun ce mahara sun hallaka wasu mute 15 a ranar Juma’a.

’Yan sanda sun tabbatar da rasuwar mutane 11 a harin da ’yan ta’adda suka kai kauyen Unguwar Lamido a Karamar Hukumar Bakori.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya karyata wani labari da ke cewa mutanen da aka kashe a harin Unguwar Lamido sun haura 40.

Sanarwar da ya fitar ta ce, “muna karyata labarin cewa da ke yawo a Facebook cewa ’yan bindiga sun kashe sama da mutane 40 a Unguwar Lamido.

“Gaskiya ne ranar Asabar 25 ga Mayu, 2024, ’yan ta’adda dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen na Unguwar Lamido, amma mutum 11 suka harbe har lahira.

“Bayan samun labarin harin DPO na babban ofishin ’yan sanda na Karamar Hukumar Bakori ya jagororin jami’ansa da hadin gwiwar ’yan banga suka kai dauki tare da dakile karuwar barnar, kuma yanzu kuma ya daidaita,” in ji sanarwar.

Gabanin sanarwar dai rahotanni sun ce mahara sun kai farmaki kan wasu ƙauyuka uku — Unguwar Lamido, Unguwar Baro da Unguwar Kare — a karamar hukumar suka kashe sama da mutane 40.

Majiyoyi sun ce maharan da suka kai farmakin a a ranar Juma’a da cikin dare sun kuma koma gidaje da dukiyoyin jama’a.

Wani shaida ya ce, “a baya ’yan bindiga sun sha yunkurin kai hari kauyen Unguwar Kare suna kasawa saboda al’ummar kauyen suna dakile su, sai a wannan karon bata-garin suka yi nasara.”

Harin Kankara

A Karamar Hukumar Kankara kuma, shaidu sun tabbatar mana cewa ’yan bindiga sun hallaka mutane 15 a yankin ’Yartaba a ranar Juma’a.

Shaidu sun ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne a sakamakon harbin kan mai uwa da wabi da ’yan ta’addan suka yi a garin.

“Mutane 15 aka kashe, yawancinsu mata ne da kananan yara; jiya aka kawo gawarwakinsu Kankara aka yi musu jana’iza,” in ji majiyarmu.

Majiyar ta ce maharan sun Bayyana a lokacin harin cewa manufarsu ita ce hana al’ummar yankin noma gonakinsu a daminar bana.