✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan siyasa sun koka da kamun ludayin sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea

Jam'iyyun siyasar kasar sun koka kan kamun bakin ludayin dakarun sojin.

A kasar Guinea, jam’iyyun siyasa sun koka bisa gazawar majalisar sojin kasar karkashin shugabancin Kanar Doumbouya da ya kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde mai shekaru 84 a watan Satumbar 2021.

Jam’iyyun siysa 58 a kasar sun fitar da wata sanarwa da ke nuna damuwa bisa rashin sanin makamar aikin sojojin kasar a karkashin shugabancin Kanar Doumbouya.

’Yan siyasar sun bayyana takaicinsu na game da tafiyar hawainiya da al’amura suke yi sakamakon rashin lakantar kamun ludayin shugabanci daga bangaren majalisar rikon kwaryar sojojin.

’Yan adawa tare da hadin gwiwar wasu jam’iyyu masu rinjaye a gwamantin da ta gabata  na fatan ganin majalisar sojojin ta fitar da jadawalin zabe a kasar.

A watan Satumbar 2021 ne sojoji suka hambarar da gwamnatin Alpha Conde, shugaban da ya mulki kasar na tsawon  shekara 10, ya kuma nemi wani sabon wa’adi bayan da ya shirya zaben jin ra’ayin jama’ar kasar.

Yanzu haka dai ana dakon sojojin su fitar da sanarwa jadawalin zaben, a yayin da shugabancin sojojin ke kokarin wanke kansa daga zargi na neman kin mika mulki tare da shirya zabe a kasar.