Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Jigawa Mista Bala Sanchi ya musanta zargin da wadansu ’yan siyasa suke yi cewa wai yana bai wa ’yan kasuwa tsaro a lokacin zaben daya gabata.
Kwamishina Sanchi ya ce maganar cewa ya janye wa dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, Malam Aminu Ibrahim Ringim jami’an tsaro, babu gaskiya a cikinta, batanci ne kawai irin na ’yan siyasa.
Ya nuna takaicinsa a kan al’amarin, inda ya ce ’yan siyasa mutane ne masu wahalar sha’ani. “Babu yadda za a yi ka yi musu daidai a rayuwa,” inji shi.
Ya ce a zaben gwamnonin da za a yi a gobe, za su samar da jam’ian tsaro 5,262 domin tattabar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
A wani labarin ’yan sanda a jihar Jigawa sun kama ’yan daba 113 a yankunan Hadeja da Kazaure da Ringim, inda suka same su da miyagun makamai. Kwamishinan ya ce duk wadanda aka kama, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace da su da zarar an kammala bincike.