Manyan manoma da ke noma mai tarin yawa ba domin bukatar cikin gidansu kadai ba sun fara hakura da sana’ar a Arewacin Najeriya saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.
A wani bincike da Aminiya ta gudanar an gano cewa da dama ’yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da ke noma a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, Abuja zuwa Jos da waɗansu yankuna na jihohin Kaduna zuwa Neja da Zamfara, Kastina da Sakkwato da Kebbi sun hakura saboda tsoron masu garkuwa da mutane.
Wani dan majalisar jihar Kaduna da ya bukaci mu sakaya sunansa ya bayyana mana cewa yana da babbar gona a birnin Gwari, da yake zuwa kafin ya zama dan majalisa, amma yanzu ya daina zuwa saboda tsoron masu garkuwa da mutane.
Ya ce ““Ba ni da zabi illa in daina zuwa gona. Kafin na shiga ofis, ina yawan zuwa duba gonar da ma’aikatana akai-akai ina ganin yadda gonar ke bunkasa, ammayanzu ba na zuwa.”
Hakazalika, Imam Hussaini Udawa, wani mai babbar gona a kan iyakar jihar Kaduna da Neja, ya yi watsi da gonarsa saboda barazanar tsoro.
Ya bayyana cewa ba ya jin dadi in ya tuna cewa ya rufe gonarsa, saboda rashin ta ya raba mutane da dama da ayyukan su.
“Rashin tsaro ya tilasta na rufe gonar da nake girbar akalla buhuna 500 a duk shekara.
“Shekara da shekaru ’yan fashi sun mamaye yankin, kuma ba ni da wani zabi illa in bar wurin,” in ji manomin.
Ya ce, ci gaba da rufe manyan gonaki na iya kara ta’azzara matsalar tsaro da kuma haifar da yunwa.
Ya kuma bayyana cewa, rufe bankunan kasuwanci da dama a jihar wata alama ce da ke nuba irin munin halin da ake ciki.
Hajiya Mairo Ahmadu, wata ma’aikaciyar gwamnati, ta ce sun shiga mawuyacin hali bayan da mahaifinta ya babbar gonarsa da ke Sakkwato saboda rashin tsaro.
Ta ce “Babbar gona ce da ake noma da kiwon shanu masu tarin yawa, ana samun nono da kayan abinci mai yawa, amma yanzu bai isa ya je gonar ba”.
Wani manomin shinkafa da ya bukaci mu sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa, bala’in rashin tsaro ya tilasta masa barin gonar shinkafarsa mai girman hekta 1,000 a Karamar Hukumar Shendam ta Jihar Filato.
Ya ce, an taba yunkurin sace shi a gonar amma Allah Ya tsare shi, daga nan bai sake koma ba, saboda tsoron abin da zai iya faruwa.
Hakazalika mun gano cewa wani kamfani da ya sayi wata babbar gona domin noman rani mai tazarar kilomita 30 daga Abuja ya yi watsi da ita saboda rashin tsaro da ke barazana ga ma’aikatansa.
A Jihar Taraba, wakilinmu ya ce, wasu manoma ’yan kasuwa da matsakaitan manoma ma duk sun hakura da noma.
Bashir Haman, wanda ke noma a kusa da Kwando a Karamar Hukumar Ardo-Kola, ya ce, rashin tsaro ya tilasta masa barin babbar gonarsa ta masara, saboda ta’addancin ’yan bindiga.
Ya ce, “Bara Allah Ne Ya kiyaye, muna gona muna shirin girbi a wata babbar gonata ta masara ’yan bindiga suka kawo mana farmaki, Allah Ne Ya kiyaye mu”.
Ya ce ” a karshe dai dole na nemi agajin ’yan farauta masu bindiga kafin muka iya girbe masarata”.
Wani masanin harkokin noma da ke zaune a Jihar Kano, Amos Banda, ya ce yawancin wuraren da ’yan bindigar suka hana noma, a nan ake samun amfanin gona mai yawa.
Ya ce, “Halin tsadar kayan abinci da ake fama da shi a yanzu ya samo asali ne daga rufe manyan gonakin kasar nan.
“Idan ana so a samu sauƙin kayan abinci, to dole a samar wa manoma tsaro domin yin noma cikin aminci.”