✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shafin karbar rancen karatu zai fara aiki ranar Juma’a —Gwamnati

Juma'a 24 ga watan nan na Mayu, 2024 shafin karbar rancen karatu ga daliban Najeriya zai fara aiki

A ranar Juma’a mai zuwa za a bude shafin neman rancen kudin karatu da Gwamnatin Tarayya ta bude domin dalibai zai fara aiki.

Manajan Daraktan Asusun Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) Mista Akintunde Sawyerr ne ya bayyana 24 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar bude shafin neman rancen kudin karatun ga dalibai.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.

Ya ce masu buƙatar rancen za su iya shiga shafin ta www.nelf.gov.ng domin neman wani agaji kuma sai su tuntubi hukumar asusun ta [email protected].

Ya ce: “Ta shafin, dalibai za su iya samun rance kudin makaranta ba tare da damuwa ba.”

Sanarwar da ke dauke da sa hannun mai kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na asusun, Nasir Ayitogo, ta ce shafin samar da rancen na da saukin sarrafawa kwarai da gaske.

Manajan Daraktan Asusun Lamunin karatun Najeriya ya shawarci wadanda suka cancanci wannan tallafi su gaggauta cikewa domin su mori tsarin da zai taimaka wa gobensu.