Dillalan shanu a Kasuwar Kara da ke garin Bukuru a Jihar Filato sun yi zanga-zangar lumana kan shirin canza musu matsuguni daga wurin da kasuwar take a yanzu.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Raya Birnin Jos (JMDB), ta ba ’yan kasuwar wa’adin makonni biyu, bisa hujjar cewa gwamnati na son ta gina filin wasa a yankin da kasuwar ta su take.
Sai dai ’yan kasuwar sun ce mayar da su yankin Gero ko Sabongida, wadanda tun zamanin tsohon gwamna David Jang a kaso mayar da su zai jefa rayuwarsu cikin hadari.
- Bala’in da matan da ’yan Bindiga suka koro ke ciki a Neja
- Yadda rashin tsaro ke hana yin noma a Arewa
Sun ce yankin da ake so a mayar da su akwai barazana mai girman gaske idan aka yi la’akari da rikicin kabilanci da addini da ya addabi jihar shekaru da dama.
Sun ce a yanzu kasuwar ta zama cibiyar hadin kai inda jama’a daga kabilu daban-daban ke haduwa domin yin kasuwanci.
’Yan kasuwar sun yi wannan roko ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a kasuwar, ranar Juma’a, karkashin jagorancin shugaban matasan kasuwar, Hamza Ahmad Yusuf.
Sun ce ba su na nufin su bijire wa umurnin gwamnati ba ne, amma suna roƙo gwamnatin ta sake tunani.
“Mu a yanzu ba muna kalubalantar matakin gwamnati bane, ko kaɗan.
“Mu abin da muke dubawa shi ne kalubalen tsaro da ke barazana ga rayuwarmu a jihar.
“Aikin gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma jin dadin jama’arta; Muna rokon a yi la’akari da halin da muke ciki, a bar mu a kasuwarmu.”