✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sintiri sun kwato matan aure biyu daga masu garkuwa a Kaduna

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan sintiri da ke kauyen Udawa a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna suka yi nasarar kama wadansu Fulani…

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan sintiri da ke kauyen Udawa a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna suka yi nasarar kama wadansu Fulani uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane, inda suka kubutar da matan aure biyu daga hannunsu.

Lamarin ya faru ne a dajin Marini da ke iyakar Udawa da Birnin Gwari bayan an sanar da ’yan sintirin cewa wadansu Fulani sun sace mata biyu a daren Litinin.

A cewar majiyar Aminiya da ke Udawa, an dade ana satar mutane a yankin kuma sai an biya kudin fansa kafin a sake su.

Amma da yake dubun wadannan ya cika sai ’yan sintirin suka yi musu kwanton bauna a cikin dajin suka kama su bayan sun sato matan daga gidajensu mazansu.

Daya daga cikin kwamandojin ’yan sintirin da ke Udawa mai suna Alhaji ya shaida wa Aminiya cewa sun kama Fulanin ne kamar kaji a cikin daji ba tare da sun sha wata wahala ba.

“Lokacin da muka samu labarin cewa sun sace matan a cikin dare da misalin karfe 11 sai muka yi musu kwantaon bauna a kan hanyarsu ta fita daga dajin da misalin karfe 3 na dare. Allah kuma Ya ba mu sa’a muka kama su kamar kaji. Ba su kuma yi musu ba domin duk sun amince aikinsu ke nan kuma sun ba da sunayen wadansu abokan ta’asarsu inda muka kama mutum daya. Mun kuma kubutar da matan biyu daga hannunsu,” inji shi.

Ya ce tuni sun mika mutanen uku ga ’yan sandan da ke garin, domin wucewa da su Kaduna. To amma kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Yakubu Sabo ya ci tura, domin bai daga waya ba, kuma bai amsa sakon tes da aka aike masa ba.