✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sintiri sun kama buhunan Wiwi 15 a Kaduna

An dai cafke su ne lokacin da ake kokarin shigar da su Karamar Hukumar Ikara

Kungiyar ’Yan Sintiri ta Jihar Kaduna ta sami nasarar cafke buhunan Wiwi guda 15 da aka yi jigilar su zuwa Karamar Hukumar Ikara da ke Jihar.

Da ya ke nuna wa manema labarai buhunan, Babban Kwamandan Shiyya na rundunar ’yan sintirin, Mallam Bala Galadima, ya ce “Wannan ba karamar nasara ba ce wajen yunkurin su na tsabtace al’umma daga shan miyagun kwayoyi.

Ya ce duk da dai wanda ake zargin shi ne mai kayan ya arce ba a sami damar kama shi ba, amma kuma sun kwace wani babur da ake zargin da shi ake safarar Wiwin.

Wasu daga cikin buhunan Wiwin da aka kama
Wasu daga cikin buhunan Wiwin da aka kama

Bala Galadima ya ce jami’anshi sun sami nasarar ne lokacin da suke suntiri a kauyen Dutsen Lungu da ke Karamar Hukumar Ikara don tsabtace yankin daga hada-hadar muggan kwayoyi.

Ya sanar da cewa sun kuma yi nasarar cafke masu sayar da kwayoyi da dama a sa’ilin wannan aiki.

Kwamandan ya ba da tabbacin cewa za su yi gaggawar mika buhunan da suka kama ga hukumar da ta kamata don ci gaba da gudanar da bincike.

Sai dai ya sha alwashin ci gaba da kokarin jami’anshi na fatattakar masu sha da safarar muggan kwayoyi a ko ina suke a fadin Jihar Kaduna don tsabtace al’umma.