Kungiyar ’Yan Sintiri ta Jihar Kaduna ta sami nasarar cafke buhunan Wiwi guda 15 da aka yi jigilar su zuwa Karamar Hukumar Ikara da ke Jihar.
Da ya ke nuna wa manema labarai buhunan, Babban Kwamandan Shiyya na rundunar ’yan sintirin, Mallam Bala Galadima, ya ce “Wannan ba karamar nasara ba ce wajen yunkurin su na tsabtace al’umma daga shan miyagun kwayoyi.
- Shan sigari na kashe ’yan Najeriya 29,000 a shekara
- An tabbatar da mutuwar mutum 22 a hatsarin jirgi a kasar Nepal
Ya ce duk da dai wanda ake zargin shi ne mai kayan ya arce ba a sami damar kama shi ba, amma kuma sun kwace wani babur da ake zargin da shi ake safarar Wiwin.
Bala Galadima ya ce jami’anshi sun sami nasarar ne lokacin da suke suntiri a kauyen Dutsen Lungu da ke Karamar Hukumar Ikara don tsabtace yankin daga hada-hadar muggan kwayoyi.
Ya sanar da cewa sun kuma yi nasarar cafke masu sayar da kwayoyi da dama a sa’ilin wannan aiki.
Kwamandan ya ba da tabbacin cewa za su yi gaggawar mika buhunan da suka kama ga hukumar da ta kamata don ci gaba da gudanar da bincike.
Sai dai ya sha alwashin ci gaba da kokarin jami’anshi na fatattakar masu sha da safarar muggan kwayoyi a ko ina suke a fadin Jihar Kaduna don tsabtace al’umma.